Buba Galadima: 'Ban san lokacin da aka haife ni ba'
A shirin Amsoshin Takardunku na karshen makon jiya, wani mai sauraronmu Jamilu Muhammad Haruna ya bukaci sanin tarihin fitaccen dan siyasar nan a Najeriya, Buba Galadima.
Kuma BBC ta tuntubi Buba Galadima inda ya ba da tarihinsa.
Wanene Buba Galadima?
Buba Galadima wanda dan siyasa ne, ya ce ba shi da tabbacin shekarun da aka haife shi sai dai ya bayyana cewa "ya kamata a ce ina da shekara 72 ko 73."
Ya fara makaranta a wani kauye da ake kira Bizzi a shekarar 1959.
A 1961 kuma ya koma Gashua inda ya kammala karatu a 1965 sannan ya tafi makarantar sakandare ta Provincial da ke Maiduguri a jihar Borno a 1966 zuwa 1970.
Daga nan ya je jami'ar Ahmadu Bello inda ya yi karatu a makarantar share fage (School of Basic Studies) inda ya fara rike shugabancin shugaban dalibai na makarantar.
"Tun daga aji daya na fara siyasa. Allah ya dora mani shugabanci tun ina karami," a cewar Buba Galadima.
Ya yi karatun digirinsa na farko a fannin injiniya na gine-ginen gidaje da hanya a shekarar 1975. Ya ce daga nan "bai ci gaba da karaunsa ba amma ya je kwasa-kwasai a kasashen waje."
Yadda ya fara siyasa
Buba Galadima ya shiga siyasa ne a 1978 ba tare da ya bar aiki ba a lokacin.
A cewarsa "ni kadai ne a jihar Borno wanda ya kawo mamba na dan majalisar wakilai na mazabarsa a zamanin NPN" kuma wannan ne dalilin da ya sa "aka bayar da sunansa domin zama minista daga jihar Borno."
"Na yi shugabancin samari na jam'iyyar NPN na kasa ina da shekara 27 zuwa 28," in ji shi.
Buba Galadima ya kara da cewa "Na kafa wata jam'iyya ni da Alhaji Abba Dabo wadda muka sanya wa suna ANC a lokacin Abacha."
Ya kara da cewa kafin lokacin Abacha an yi jam'iyyar NRC kuma "ni ne sakataren kudi na jam'iyyar."
Buba Galadima ya ce "ba ni da mai gida a harkar siyasa. Kullum gashin kai na nake ci, a tsaye nake a kan kafata domin ina da ra'ayi kan duk wani abu na rayuwa."
"A Najeriya, idan kana da mai gida ba ka da ra'ayi sai na mai gidanka. Wannan ita ce babbar matsalata a zama wani abu a siyasar Najeriya," kamar yadda Buba Galadima ya bayyana.
"Ina daya daga cikin mutumin da ya ba da miliyan daya na farko domin kafa jam'iyyar APP. Dan uwana Alhaji Umaru Shinkafi kuma yana daya daga cikin fitilun jam'iyyar APP har ta koma ANPP."
Matsalata da shugabanni

A cewar Buba Galadima kasancewarsa mai ra'ayi a kan duk wani batu ne ya sa ba shi da farin jini wajen shugabanni a Najeriya.
Ya kara da cewa "Dukkan mutumin da ba zai kwantar da kai idan an ce masa Allah 10 ne ya ce eh ba, toh ba zai samu farin jini a wajen shugabanni irin na Najeriya ba."
Buba Galadima ya bayyana cewa "an tuhume ni ko kulle ni ko ja mani kunne ko an sa mani ankwa an sa ni a karkashin kasa sau 38."
Ya ce an fara kulle shi a 1984 a zamanin mulkin soja na Shugaba Buhari.
'Alakata da Buhari'
Buhari na daya daga cikin mutanen da nake ganin girmansu a ido na.
Mun fara mu'amala da shi tun yana gwamnan Borno, amma "shi ba zai iya tunawa ba amma ni da yake ina karamin jami'i zan iya tunawa."
Buba Galadima ya ce sun fara harkar siyasa da Buhari tun shekarar 2002 bayan Buharin ya shiga jam'iyyar APP a lokacin.












