Yadda ta kaya a gasar kofin FA

Manchester City ta yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na hudu na gasar cin Kofin Kalubale, bayan da ta doke Port Vale da ci 4-1.
City ta lashe duka kofuna hudu na cikin gida a bara, to amma a bana tana fuskantar babban kalubale a gasar Firimiya daga Liverpool.
City ta saka wa bakin kwallayen hudu ne ta hannun Phil Foden da Sergio Aguero da kuma Oleksandr Zinchenko.
A minti na 58 ne kuma dan wasan Port Vale Taylor Harwood-Bellis ya ci gida.
To sai dai makwabtan City din wato Manchester United wadda a baya ta lashe kofin na FA sau goma sha daya ta yi canjaras ba ci 0-0 da Wolverhampton.
A karon farko cikin shekara biyar, United ta kammala wasa ba tare da buga wa mai tsaron raga kwallon da ya ture ba.
Ita ma Leicester ta doke Wigan ne 2-0, yayin da Bournemouth ta casa Luton 4-0
Ga dai yadda sakamakon kungiyoyin da ke Firimiya ya kasance.
Wolves 0-0 Manchester United
Preston 2-4 Norwich
Burnley 4-2 Peterborough
Southampton 2-0 Huddersfield
Bournemouth 4-0 Luton
Leicester 2-0 Wigan
A ranar Lahadi Liverpool za ta karbi bakuncin makwabciyarta Everton a ci gaba da gasar cin kofin na kalubale.
To sai dai kafin nan Chelsea za ta kara da Nottingham Forest, inda Tottenham za ta kece raini da Middlesbrough.











