Sojojin Chadi da ke yaki da Boko Haram a Najeriya sun janye

Asalin hoton, Getty Images
Chadi ta janye dakarunta da ke yaki da kungiyar Boko Haram daga kan iyakarta da Najeriya.
Kasar na daga cikin kasashen rundunar hadin gwiwa tare da Najeriya da Nijar da Kamaru masu makwabtaka domin yakar kungiyar mai kai hare-hare a yankin iyakokin kasashen.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito kakakin rundunar sojin Chadi, Kanar Azem Bermandoa yana cewa sojojin sun kammala aikinsu kuma dukkansu za su koma gida.
Jami'in ya ce sojojin za su koma wuraren aikinsu a tabkin Chadi amma bai bayyana ko za a maye gurbinsu da wasu ba.
Sai dai babban hafsan tsaron kasar, Janar Tahir Erda Tahiro ya ce idan har kasashen rundunar hadin gwiwar sun amince da kafa wata rundunar to akwai yiwuwar za a sake tura wasu sojojin.
Akalla mutum 35,000 ne aka kashe a Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi sakamakon rikicin Boko Haram da ya samo asali daga Najeriya a shekarar 2009.
Yanzu kungiyar ta yi mubaya'a ga kungiyar ISWAP, wadda ke addabar yankin da take da sansanin horas da mayaka a iyakokin Nijar kuma take yawan kai hare-hare a kan sojojin yankin.
A watan Disamban da ya gabata kungiyar ta kashe mutum 14 baya ga wasu mutum 13 da suka bace a harin da ta kai wa wani kauye a yammacin Chadi.
Kasashen yankin sun yi hadin gwiwar ne domin yakar kungiyoyin tare da 'yan sa-kai, dalilin da ya sa Chadi ta bayar da gudummawar soja 1,200.
Yanzu an janye dakarun daga fadin yankin, inda za a "tura su zuwa tabkin Chadi domin tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar," inji wani jami'i.
Kamaru ta ce tana yaki da sake bullowar mayakan Boko Haram, yayin da rahoton kungiyar Amnesty International ke cewa an kashe mutum 277 a kasar, cikinsu har da fararen hula 225 a shekarar 2019.











