'Yan makaranta 12 sun mutu a harin bam a Burkina Faso

Burkina Faso na yaki da 'yan ta'adda

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Burkina Faso na yaki da 'yan bindiga

Akalla mutum 12 sun mutu bayan wata motar 'yan makaranta ta taka nakiya a yankin arewa maso yammacin Burkina Faso.

Nakiyar ta tashi ne lokacin da motar 'yan makarantar ke wucewa a yankin Teoni, a cewar jami'an tsaro, a cewar rahoton gidan rediyon Omega na kasar.

Tashin bam din ya hallaka akalla mutum 12 yawancinsu kananan yara. Yaran na hanyarsu ta komawa makaranta ne daga hutu lokacin da abin ya ritsa da su.

Wasu kafafen yada labaran kasar sun ce adadin ya kai mutum 14. Hukumomi ba su riga sun fitar da alkaluma ba tukuna.

Sojoji uku da mayakan sa-kai 20 ne suka mutu a wani hari da aka kai wa sansanin sojin yankin.

Tashin bam din na zuwa ne kwana daya da kashe 'yan bindiga 10 da suka kai wa 'yan sintiri hari a lardin Soum da ke kudancin kasar.

An samu karuwar hare-haren masu tayar da kayar baya a kasar masu alaka da kuniyar al-Qa'ida da IS a cikin 'yan makonnin nan.