Rikicin Hong Kong ya ritsa da jami'in jakadancin China

Asalin hoton, Getty Images
China ta sallami daraktan karamin ofishinta a Hong Kong Wang Zhimin.
Gwamnatin China ta sallami mista Wang ne sakamakon zanga-zangar da masu goyon bayan demokuraddiyya a Hong Kong suka shafe wata shida suna yi.
Ayyukan masu zanga-zangar sun fusata hukumomin China har ta kasa yin hakuri da wasu jami'an gwamnatin kasar da ke Hong Kong.
Kamfanin dillacin labarai na Xinhuwa ya ce yanzu sakataren jam'iyyar Communist Party a lardin Shanxi Luo Huiningan ne ya maye gurbin mista Wang.
Sai dai Carrie Lam ta ci gaba da zama shugabar Hong Kong da goyon bayan gwamnatin China, duk da cewa kudurin dokar da ta gabatar ne ya haddasa zanga-zangar a watan Maris na 2019.
Dokar za ta ba da damar tisa keyar wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka daga Hong Kong zuwa China.
Hakan ya haifar da fargabar cewa sabuwar dokar na iya bayar da damar wuce gona da iri wurin tsare masu adawa da gwamnati da kuma kawar da su daga yankin.

Asalin hoton, Reuters
Masu zanga-zangar sun tarbi ranar sabuwar shekara da wani maci da dubban masu goyon bayan demokuradiyya suka halarta.
Sai dai an dan samu hatsaniya a yayin zanga-zangar lumanar.
'Yan sanda sun yi amfani da motocin ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye da harsasen roba domin tarwatsa masu zanga-zangar.
A ranar jajiberin sabuwar shekarar ne 'yan majalisun dokoki da manyan mutane sama da 40 daga kasa 18 suka aike wa Carrie Lamp sakon neman ta bi sahihan hanyoyi wajen biyan bukatun mutanen Hong Kong.
A shekarar 1997 ne ikon Hong Kong ya koma hannun China daga hannun Birtaniya karkashin tsarin 'kasa daya, mai amfani da tsarin shugabanci biyu".
Abin nufi shi ne Hong Kong yankin kasar China ne, amma tana da nata dokokin da iyakokin kasa da kuma 'yanci da hakkoki.
Hakkokin sun hada da 'yancin gudanar da taruka da 'yancin fadin albarkacin baki.











