A ranar 9 ga watan Yunin 2019ne, aka fara wata zanga-zanga mafi muni a Hong Kong- ana zanga-zangar ne domin nuna kin amincewa da shirin sauya dokar hukunta mai laifi a wata kasar.
Kudurin Dokar dai zai bayar da damar tasa keyar mai laifi zuwa wata kasar domin ya fuskanci hukunci, har ma a wuraren da Hong Kong ba ta kulla yarjejeniya makamanciyar wannan ba.
Ma'anar hakan dai shi ne za a rinka tura wadanda suka aikata laifi a Hong Kong zuwa China domin fuskantar hukunci, wannan ya sa masu zanga-zangar ke ganin idan aka yi hakan ba lallai ne a yi musu adalci a shari'ar da za a yi musu ba.
Kimanin watanni shida ke nan, an ajiye dokar, amma kuma har yanzu al'ummar Hong Kong a fusace su ke a kan dokar, inda yanzu suka karkata suna huce takaicinsa a kan gwamnati da kuma jami'an tsaro.
Ga wasu daga cikin hotunan da suka dauki hankali a tsawon watanni shidan da aka shafe ana zanga-zangar a Hong Kong.
Asalin hoton, STR
Bayanan hoto, Bayan mummunar zanga-zangar ta farko da aka yi, gwamnatin Hong Kong ta ce za ta soke dokar, amma kuma hakan bai gamsar da 'yan adawa. A ranar 16 ga watan Yunin 2019 ne, masu zanga-zanga miliyan biyu suka fito inda suka nemi a soke kudurin dokar.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, A ranar 1 ga watan Yuli, a daya daga cikin ranakun da aka gudanar da zanga-zanga, daruruwan masu zanga-zangar sun kutsa kai cikin fadar gwamnatin Hong Kong. Sun mamaye ginin fadar a cikin dare inda suka rinka wake-wake tare da lika takardu a jikin bangon ginin wadanda suka kunshi kalamai na rashin amincewa da kudurin gwamnatin.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Bayan shafe wata guda ana zanga-zangar, wasu masu zanga-zanga masu zafin kai da ake kira hardcore group su ka bullo. Suna sanye ne da bakin kaya inda suka boye kamanninsu, suna taho-mu gama da 'yan sanda.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yayin da 'yan sanda su ka fara amfani da dabarun tarwatsa masu zanga-zanga, alaka tsakaninsu ta kara tabarbarewa. Wasu daga cikin masu zanga-zangar na zargin cewa 'yan sanda na cin zalinsu inda su ke so a gudanar da cikakken bincike a kan zargin.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Wani abu da ya ja hankali a zanga-zangar, shi ne yadda wasu maza sanye da fararen riguna ke kai wa masu wucewa hari a Yuen Long. 'Yan sanda sun yi jinkirin zuwa wajen, lamarin da ya haifar da zargin cewa jami'an tsaron na sane shi ya sa suka jinkirta zuwa wajen domin kawo dauki.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A farkon watan Satumbar 2019 ne, 'yan sanda suka fara amfani da sabbin dabaru ciki har da watsa wani ruwa mai launin shudi a kan masu zanga-zangar, ma'anar hakan ita ce ko da masu zanga-zangar sun gudu za a iya gane su. An dai kama dubban mutane a cikin watanni shidan da ake zanga-zangar.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Zanga-zangar ta shafi kusan ko'ina a Hong Kong inda ta janyo asara da dama. Nan wata zanga-zangar lumana ce da aka yi a wani katafaren shago da ke Sha Tin.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Bangon Lennon, ya zamo wata matattarar rubuta sako tare da mannewa a jiki ga masu zanga-zangar
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Wannan matar, tsohuwa ce wadda ake ganin ta girmi mafi yawancin masu zanga-zangar, ta daga tutar Birtaniya ta kuma shaida wa manema labarai cewa tana mai matukar tunani a kan abin da zai faru ga birninsu nan gaba, don haka tana matukar kewar zamanin mulkin turawa.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Daya daga cikin masu zanga-zanga ya bukaci gwamnati da ta daina ayyana zanga-zangar a matsayin tashin hankali, inda ya bayar da misalin cewa duk da yawan cuncurundon mutane sun bai wa motar daukar marasa lafiya dama ta wuce.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Masu zanga-zanga sun kebe kansu a wata makaranta har tsawon kwana da kwanaki inda suke watsa wa 'yan sanda fetur.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Yawancin abubuwan da su ka rinka faruwa a Hong Kong, sun sanya alamun tambaya a zukatan mutane, inda wasu ke ganin me ya sa masu zanga-zangar su ka sadaukar da rayuwarsu da kuma 'yan cinsu. Yawancinsu dai na ganin rayuwarsu a nan gaba na cikin hadari.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Watanni shidan da aka shafe ana zanga-zanga, sun nuna cewa, al'ummar birnin za su iya kai wa makura wajen kare martabarsu da kimarsu gami da 'yancinsu.