Yadda aka yi juyayin mutuwar Janar Soleimani a Iraki

Bayanan bidiyo, Masu makoki sun zagaye motar da ke dauke da gawar Qasem Soleimani

Dubun dubatar masu tattaki a Iraqi sun la'anci Amurka saboda kashe kwamandan sojin Iran Janar Qasem Soleimani a wani harin sama ranar Alhamis a Iraki.

Masu tattakin zagaye da gawar Qasem Soleimani sun zagaya manyan titunan Baghadaza a safiyar ranar Asabar. Tattakin ne ke kaddamar da zaman makokin rasuwar Janar Soleimani.

Qasem Soleimani shi ne kwamandan rundunar sojin Iran mai suna Quds Force, wadda ke ayyukanta a kasashen waje a yankin Gabas ta Tsakiya.

Za a mayar da gawarsa zuwa Iran, inda za a binne shi a kauyensu.

Masu zaman makokin sun kuma yi juyayin mutuwar Abu Mahdi al-Muhandis, kwamandan rundunar Kataib Hezbollah.

Abu Mahdi al-Muhandis dan asalin Iraqi, shi ne kwamandan mayakan sa-kai da Iran ke goyon baya a cikin Iraki.

Tun da sanyin safiyar ranar Asabar ne masu tattakin suka yi dafifi dauke da hoton Soleimani da jagoran addini Iran Ayatollah Ali Khamenei da kuma tutocin Iraqi da na mayakan sa-kai, suna yin wakokin la'antar Amurka.

Rahotanni na cewa a yammacin ranar Asabar ne za a tafi da gawar Soleimani Iran, wadda ta riga ta ayyana zaman makokin kwana uku saboda kisan janar din nata.

A bangare guda kuma, wasu 'yan Iraqi sun yi tattaki a wasu titunan Baghadaza domin murnar samun labarin mutuwar Soleimani.

Ana zargin marigayi Soleimani da kitsa murkushe zanga-zangar masu rajin dimokuradiyya a baya-bayan nan.

Yadda masu makoki suka zagaye motar da ke dauki gawar kwamandan sojin Iran Janar Qasem Soleimani

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu makoki sun zagaye motar da ke dauke da gawar Qasem Soleimani

Yanzu abin da shugaban Iran ya mayar da hankali a kai shi ne isar da wani kakkarfan sako da zai nuna yadda janar din ke da muhimmaci ga gwamnatin kasar.

Soleimani shi ne jami'in sojin Iran mafi muhimmanci a Iraki kuma jami'in tara bayanan sirri na soji mafi muhimmanci.

Yanzu shugaban na neman ganin irin manyan gangamin da za a gudanar game da kisan Soleimani a manyan titunan kasar domin nuna Soleimani a matsayin gwarzo kuma shahidi.

Presentational grey line

Wane ne Janar Qasem Soleimani?

Qasem Soleimani na daya daga cikin mutane da ke da tasiri a Gabas ta Tsakiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Qasem Soleimani na daya daga cikin mutane da ke da tasiri a Gabas ta Tsakiya

Mai shekara 62 da haihuwa, Janar Soleimani ya jagoranci fitattun sojojin Qurdawa wadanda Amurka ta zarga da shirya kai hare-hare kai tsaye ko kuma ta hanyar hanyoyin da suke kusa da su - a cikin nahiyoyi biyar na duniya.

Shugaba Donald Trump ne ya bayar da umarnin kai harin bayan wasu hare-hare na baya-bayannan kan ofishin jakadancin Amurka a Iraki wanda aka dorawa mayakan da ke samun goyon bayan Iran.

Suna da shahara a Iran

Wasu na girmama kwamandan, wasu sun ƙi shi, da kuma sauran bayanai da ake wallafawa game da Janar Soleimani.

Rahotanni na cewa Soleimani ya na da kusanci da jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Rahotanni na cewa Soleimani ya na da kusanci da jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei

Ya fara shahara ne a baya-bayannan inda yake jagorantar ayyuka domin yin suna da samun karbuwa a Iran, inda kuma ake bada rahoto game da shi a kafafen yada labarai.

Yadda ya shahara zuwa matakin babban kwamanda

Ana tunanin Soleimani ya taso ne a gidan da ba masu kudi ba sannan yana da karancin ilimin boko.

Sai dai Soleimani Amma ya yi suna cikin sojojin Juyin Juya Halin - wadanda suka yi fice a Iran kuma an ruwaito su suka fi kusa da Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei.

Ya yi suna a lokacin yakin da aka yi tsakanin Iran da Iraki tsakanin 1980 zuwa 1988 daga nan kuma ya samu karin matsayi zuwa babban kwamanda.

Bayan ya zamo jagoran dakarun Qurdawa a 1998, Soleimani ya yi kokarin fadada tasirin Iran a gabas ta tsakiya ta hanyar jagorantar hare-hare tare da samar da makamai ga kawaye da kuma bunkasa mayakan dake bai wa Iran goyon baya.

Soleimani ya taimaka wa 'yan Shi'a da kungiyoyin Kurdawa a Iraqi da ke yaki da Saddam Hussein da wasu kugiyoyi a yankin har da kungiyar Hezbollah a Lebanon da Hamas a yankunan Palastinawa.

Qassem Soleimani (hagu) lokacin wasu jerin hare-hare kan mayakan IS a 2015

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Qassem Soleimani (hagu) lokacin wasu jerin hare-hare kan mayakan IS a 2015

Bayan Amurka ta mamaye Iraki a 2003, Soleimani ya fara bai wa mayaka umarnin kai hare-hare kan dakarun Amurka da sansanin sojojin Amurkan, lamarin da ya halaka daruruwa.

An kuma ce ya samar da wata dabara ga Shugaban Syria, Bashar al-Assad domin mayar da martani kan tawayen da aka yi masa a 2011.

Tallafin da Iran da Rasha suka ba shi ya sa lamura sun sauya kan 'yan tawayen abin da ya bai wa gwamnatin damar kwace mahimman birane da yankuna.

Tasirin Soleimani a yaki da mayakan IS a Iraki Key

A wasu lokutan an sha ganin Soleimani da kan shi a jana'izar 'yan Iran da Syria da Iraki suka kashe.

Ya na kuma da tasiri a a yakin da aka yi da kungiyar IS a Iraki.

Iran ta taimaka wajen bada makamai da horas da dakaru abin da ya taimaka wajen samun galaba kan IS amma da yawan 'yan Iraki na ganin kamar mulkin mallaka Iran din ta yi.

Mayakan Iraki sun yaki IS

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mayakan Iraki sun yaki IS

Sai dai karbuwar da Soleimani ya samu ta wuce gabas ta tsakiya.

A 2011, an zargi dakarun Kurdawa da hannu a shirya kisan jakadan Saudiyya aAmurka ta hanyar jefa bam a wani gidan cin abinci a Washington.

Bayan shekara biyu kuma, wata kotu a Jamus ta samu wani sojin Kurdawa bisa samunsa da yiwa tsohon shugaban kungiyar (German-Israeli group) da mutanen da ke kusa da shi leken asiri.

A Aprilun 2019, Saakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya sake sauyawa dakarun juyin juya hali da dakarun Kurdawa fasali.

Zama barazana ga Amurka

Abubuwan da suka faru sun kasance kan gaba a Iraki sakamakon hare-haren ramuwar gayya tsakanin sojojin Amurka da dakarun da ke samun goyon bayan Iran.

A ranar Lahadi, Amurka ta kaddamar da wasu hare-hare a Iraki da Syria kan mayakan Iraki da ke samun goyon bayan Iran wanda kuma aka dora wa Iran din alhakin harin da ya kashe wani farar hula dan Amurka.

An kashe Janar Qasem Soleimani sakamakon wani harin sama kusa da filin jirgin saman Bagadaza.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An kashe Janar Qasem Soleimani sakamakon wani harin sama kusa da filin jirgin saman Bagadaza.

Wasu fusatattun jama'a sun yi ba dai dai ba a wani wajen cin abinci da ke ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza abin da ya sa dakarun Amurka harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa su.

An kuma tura wasu karin dakarun Amurka zuwa yankin domin kare sansanonin sojoji amma mutane kalilan ne suka yi tsammanin irin haka za ta faru kan wani babban jami'i a Iran.

Cikin wata sanarwa, ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce Soleimani ya dade "yana bijiro da tsare-tsaren kai wa jakadun Amurka hari a Iraki da kuma sauran sassan yankin".

"Janar Soleimani da dakarun Kurdawa su ne suka kashe daruruwan Amurkawa tare da raunata wasu da dama," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sai dai wasu a Amurka sun yi ayar tambaya kan matakin.

Daya daga cikin mayan 'yan takarar da ke zawarcin kujerar shugaban kasa a Amurka kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Joe Biden ya wallafa a Twitter cewa harin ''babbar alamar takalar fada ne" kuma ya ce Shugaba Donald Trump ya tsokano fada ne".

"Muna iya kasnacewa dab da fadawa wani babban rikici a sassan gabas ta tsakiya".