Soleimani: Faransa na neman kawar da rikici a yankin Gulf

Abin da ya rage daga harin da Amurka ta kai wa tawagar motocin Soleimani

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Abin da ya rage daga harin da Amurka ta kai wa tawagar motocin Soleimani

Shugaban Faranasa Emmanuel Macron ya tattauna matsalar zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya tare da takwaransa na Iraki Barham Salih da yarima Sheikh Mohammed bin Zayed al-Nahyan na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sanarwar da ofishin Macron ya fitar ta ce shugaban da takwaransa na Iraki za su ci gaba da aiki tare domin kawar da barkewar rikici a Iraki da yankin Gabas ta Tsakiya.

Tattaunawar shugabannin ta ranar Asabar ta biyo bayan macin da dubban mutane suka yi domin juyayin kashe kwamandan sojin Iran a kasar, Qassem Soleimani.

Harin da Amurkan ta kai da jirgi mara matuki ya kuma yi sanadaiyar mutuwar kwamandan mayakan sa-kai da Iran din ke goyon baya a Iraki mai suna Abu Mahdi al-Muhandis.

Harin na birnin Baghadaza ya tayar da kura tare da fargabar yiwuwar barkewar wani sabon rikici a yankin Gulf.

Amurka ta ce ta kashe Janar Soleimani domin kauce wa yaki. Gwamnatin Shugaba Trump ta bayyana marigayin a matsayin wanda ya kitsa hare-haren da Iran ke kaiwa.

A nata bangaren, Iran ta yi alkawarin daukar "mummunar fansa" a kan kisan babban jami'in sojin nata.