Soleimani: Faransa na neman kawar da rikici a yankin Gulf

Shugaban Faranasa Emmanuel Macron ya tattauna matsalar zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya tare da takwaransa na Iraki Barham Salih da yarima Sheikh Mohammed bin Zayed al-Nahyan na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sanarwar da ofishin Macron ya fitar ta ce shugaban da takwaransa na Iraki za su ci gaba da aiki tare domin kawar da barkewar rikici a Iraki da yankin Gabas ta Tsakiya.

Tattaunawar shugabannin ta ranar Asabar ta biyo bayan macin da dubban mutane suka yi domin juyayin kashe kwamandan sojin Iran a kasar, Qassem Soleimani.

Harin da Amurkan ta kai da jirgi mara matuki ya kuma yi sanadaiyar mutuwar kwamandan mayakan sa-kai da Iran din ke goyon baya a Iraki mai suna Abu Mahdi al-Muhandis.

Harin na birnin Baghadaza ya tayar da kura tare da fargabar yiwuwar barkewar wani sabon rikici a yankin Gulf.

Amurka ta ce ta kashe Janar Soleimani domin kauce wa yaki. Gwamnatin Shugaba Trump ta bayyana marigayin a matsayin wanda ya kitsa hare-haren da Iran ke kaiwa.

A nata bangaren, Iran ta yi alkawarin daukar "mummunar fansa" a kan kisan babban jami'in sojin nata.