Real Madrid: Hazard ba zai buga Super Cup ba a Saudiyya

Real Madrid za ta yi tattaki zuwa kasar Saudiyya a mako mai zuwa domin buga gasar Supercopa ba tare da Eden Hazard ba yayin da yake ci gaba da murmurewa daga raunin da ya ji.

Zinedine Zidane ne ya tabbatar da hakan a wurin taron manema labarai gabanin wasan Madrid da Getafe, inda ya ce dan wasan bai dawo atasaye ba.

Madrid za ta barje gumi da Valencia ranar Laraba a gasar Spanish Super Cup a filin wasa na Rey Abdullah de Yeda na kasar Saudiyya.

"Hazard ba zai buga Supercopa ba, ina fatan zai murmure nan gaba kadan," in ji Zidane.

Hakan na nufin Hazard zai ci gaba da zama a benci har nan da kwana 10 masu zuwa sakamakon raunin da ya ji tun a watan Nuwamba a wasan Paris Saint-Germain a filin wasa na Bernabeu.

Kazalika ba zai buga wasan da Madrid din za ta yi da Getafe ba na La Liga mako na 19 a yau Asabar.

Dan wasan na kasar Belgium kwallo daya kacal ya ci a kakar bana cikin wasa 13 da ya buga wa Real Madrid.