Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lafiya Zinariya: Tsangwamar da mata marasa haihuwa ke fuskanta
Latsa alamar lasifika domin sauraron shirin
A wannan makon Habiba Adamu ta tattauna da wasu mata kan matsalar rashin haihuwa da ke ci wa ma'aurata musamman mata da dama tuwo a kwarya.
Batun rashin haihuwar dai na daga wa maza hankali, al'amarin da a wasu lokutan ke janyo rabuwar aure.
A arewacin Najeriya da jamhuriyar Nijar da ma sauran kasashen Afirka matar da ba ta haihuwa kan samu matsala da dangin mijinta.
An samu yanayi da dama da iyayen maza kan umarci 'ya'yansu da su rabu da matar da ba ta haihuwa ko kuma su sa 'ya'yan nasu kara aure ko a dace.