An dakatar da jami'an gidan yari kan mutuwar fursunoni

Hukumomi a Najeriya sun ce an dakatar da wasu ma'aikatan gidan yari takwas bayan da wutar lantarki ta kashe wasu fursunoni a wani gidan yari a jihar Legas.

A wata sanarwa, kakakin gidan yarin ya ce dakatarwar za ta ba su damar yin bincike kan lamarin yadda ya dace.

Ranar Litinin ne dai wasu fursunoni biyar suka mutu bayan da aka kawo wuta mai karfi a gidan yarin na unguwar Ikoyi ta jihar Legas.

Daya daga cikin ma'aiktan gidan yarin ya shaida wa BBC cewa wata waya ce da ta tsinke ta fado kan gadon da fursunonin ke kwance suna barci.

Ministan harkokin cikin gidan Najeriya, Rauf Aragbesola ya ziyarci gidan yarin kuma ya shaida wa manema labarai cewa duk wanda aka kama da hannu ko kuma sakaci da aiki a gidan yarin zai fuskanci shari'a.