An gafarta wa fursunoni 2,000 a Rwanda

Gwamnatin Rwanda ta gafarta wa fursunoni 2,000, cikin su har da jagorar 'yan hamayya.

Victoire Ingabire, 'yar jam'iyyar FDU-Inkingi, tana wa'adin shekara 15 a daure bisa laifin yi wa jami'an tsaro barazana da kuma kaskantar da kisan kare-dangi na 1994.

Tana cikin manyan masu hamayya da Shugaba Paul Kagame kuma ta ce daurin da aka yi mata na da alaka da siyasa.

Mr Kagame ya sha yabo saboda sauye-sauyen da ya kawo wa tattalin arzikin kasar ko da yake yana shan suka bisa take hakkin dan adam.

Ya lashe zabe karo na uku da kashi 98.8 cikin 100 a zaben da aka yi a bara, ko da yake masu sa ido sun ce an tafka magudi a zaben.

A zaben 'yan majaliar dokokin da aka yi a watan Satumba, 'yan hamayya biyu daga jam'iyyar Democratic Green sun yi nasara a karon farko.

An bayyana sakin Ms Ingabire da sauran fursunoni 2,140 bayan taron kwamitin zartarwar kasar.

Ba a fadi dalilin sakin nasu ba, sai dai wata sanarwa ta ce Mr Kagame ya dauki matakin ne a matsayin wani jinkai na shugaban kasa.

An saki mawakiin nan Kizito Mihigo wanda aka yi wa daurin shekara 10 tun daga shekarar 2015 saboda zargin kitsa kashe Shugaba Kagame.

Ms Ingabire ta yi murmushi lokacin da ta fita daga gidan kurkuku, sanye da riga mai launin tutar jam'iyyarta.

Ta gode wa shugaban kasar sannan ta yi fatan cewa sakin nata zai zama silar bude fagen siyasa a kasar Rwanda.