Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Jami'an tsaron Habasha sun ci zarafin Fursunoni'
Wani sabon rahotan kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) ya zargi jami'an tsaron Habasha da aikata fyade da azabtarwa kan fursunonin siyasa a gidan yarin jihar Somali da ke gabashin kasar.
HRW ta tattara shaidunta ne a tattaunawar da ta yi da mutum sama da 100 da aka tsare a gidan yarin na Ogaden tsakanin 2011-2018.
Maria Burnett ta HRW ta ce, rahotan na dauke da cikakkun bayanai kan cin zarafin da aka aikata a tsawon shekaru kan fursunoni.
Ta kuma bayyana yadda ake musu tsirara da lakada musu dukan tsiya a gaban sauran mutanen da ake tsare dasu.
Matan kuma da suma ke tsare, sun bayyana yadda suke haihuwa a gidan yari sakamakon fyade da masu gadin fursunan suka yi musu.
Rahotan na HRW ya kuma ce akasarin fursunonin mutane ne da ke jiran ayi musu shari'a.