Me ya sa 'yan Najeriya ke rububin zuwa Dubai?
- Marubuci, Daga Faith Oshoko
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Pidgin
An dade da 'yan Najeriya ke nikar gari zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa domin wani sha'ani.

Asalin hoton, Instagram/@davidooficial
Shekaru da dama kenan da 'yan Najeriya ke nikar gari zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa domin yin hutu ko halartar bukukuwa.
A wannan shekarar bikin kalankuwar mawaka za a yi a karo na uku, sai kuma bikin biyu daga cikin mutanen da suka taba yin zaman dabaron wata uku a gidan Big Brother Nigeria, wato Bam Bam da Teddy A.
Don haka muke son sanin wai meye a kasar Hadaddiyar Daular Larabawar nan da ake ta turuwa cikinta?
Farashi
Shugaban kamfanin shirya tafiye-tafiye Irinajo Nigeria Adedamola Idowu, ya shaida wa sashen BBC Pidgin cewa da dan kudi kalilan za ka iya zuwa Dubai.
"Ya danganta da lokacin da kake son yin tafiyar. Zan iya tunawa lokacin da na tafi Dubai a watan Satumba, na kashe dala 1,076, kwatankwacin naira 390,000, shi ne kudin kwana biyar a otal da tikitin jirgi, da yawon da aka yi da ni a cikin gari.
"Amma idan lokacin Kirsimati ne wato watan Disamba za ka kashe dala 1,380 kwatankwacin naira 500,000," in ji Idowu.
Sayayya
Sayayyar kayayyaki na daga cikin abin da 'yan Najeriya ke zuwa yi Dubai, inda akan ce wai farashin gwal na da sauki a kasar.
A nan ma, Adedamola ya bayyana lokutan da ya fi dacewa don yin sayayya a Dubai.
"Lokacin da za ka samu kaya da arha shi ne 26 ga watan Disamba, zuwa karshen watan Janairu, saboda akwai abin da suke yi a lokacin wato lokacin baje koli a Dubai, a wannan lokaci suna karya darajar kayayyakinsu.''
Ya kara da cewa kasuwanci na garawa sosai a kasar, idan ka shiga Deira kuwa tamkar kana Najeriya don nan ce matattararsu.

Asalin hoton, Instagram/@mercyeke
Biza
Babu takamaimai adadin 'yan Najeriya da ke zuwa Dubai, wata kididdiga ta nuna sama da mutum miliyan 15 ne daga sassa daban-daban na duniya suka shiga kasar a shekarar 2018.
Daya daga cikin dalilan shi ne izinin shiga kasar ba ta da wahalar samuwa, kuma kana kwance a daki za ka iya shiga intenet don shigar da ita.
Mista Idowu ya yi karin haske kan batun samun biza "Ban taba jin labarin Dubai sun hana wani bizar shiga kasarsu ba, in dai kana da kudi sannan ba ka da tarihin aikata mugun laifi.''

Asalin hoton, Intagram/@tobibakare
Daukar kayatattun hotuna
Ba Bam Bam da Teddy A ne kadai ke zuwa Dubai don yin shagalin bikin aure ba, mutane da dama na zuwa, misali lokacin da fitaccen mawaki Two Face da aka fi kira da 2baba ya auri mai dakinsa Annie, a can Dubai aka yi.
Don haka BBC ta tambayi Adedamola me ye dalilin da ya sa ake hakan?
"Dubai tana da abubuwan more rayuwa da yawa, kuma akwai wurare masu kayatarwa da in dai ka dauki hoto a wurin, mutane za su fara tambayarka ina ka dauki hoton nan, don haka mutane ke zuwa don shakatawa da kashe kwarkwatar idonsu.''











