Kun san abin da Buhari zai je yi Rasha?

President Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

A ranar Litinin ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Rasha don halartar taron kasashen Afirka da Rasha da za a yi.

Za a shafe kwana uku ana taron ne wanda zai fara daga ranar 23 zuwa 25 ga watan Oktoba.

Manyan abubuwan da Shugaba Buhari zai mayar da hankali wajen tattauna su a Rasha sun hada da tsaro da kasuwanci da zuba jari da fasaha da samar da iskar gas.

Shugaban zai kuma gana da takwaransa na Rasha Shugaba Vladimir Putin, don ganin yadda za su kulla dangantaka mai karfi kan wadancan bangarori.

Hakan zai kara karfin abin da Najeriya ke son cimma a bangaren masana'antar iskar gas.

Taron, wanda shugabannin kasashen Afirka za su halarta zai samar da manufofi kan batutuwan da duniya ke mayar da hankali a kai kamar fasaha da bunkasar makamashi da hakar ma'adanai da karafa fasahar tsaro da noma da kuma ababen more rayuwa.