Buhari ya yi Allah wadai da sace yaran Kano

TWITTER/GARBA SHEHU

Asalin hoton, TWITTER/GARBA SHEHU

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa rundunar 'yan sandan kasar kan kokarin da suka yi wajen gano masu satar yara a Kano da kuma gidajen sauya dabi'u ''na bogi'' a Kaduna da Katsina.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Mallam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya yi kira ga 'yan sandan su ci gaba da irin wannan kokarin da suke yi a fadin kasar.

Shugaban ya bayyana cewa wannan samamen da 'yan sandan suka kai, ya zo daidai da kudirinsa na kare hakkin bil adama da kuma kare mutuncin al'umma ba tare da la'akari da shekarunsu ko addini ko kuma kabila ba.

Sanarwar ta ce shugaban ba zai goyi bayan ko wane irin laifi da ya saba doka ba ciki kuwa har da garkuwa da kananan yara tare da sayar da su.

Shugaban ya ce kan batun azabtarwa kuma, '' a wannan zamanin babu wata gwamnatin dimokradiyya da za ta amince da kasancewar gidajen azabtarwa da ake cin zarafin wadanda aka kulle da sunan gyaran tarbiyarsu.''

Ya kuma yi kira ga jama'ar kasar baki daya da su sa ido su kuma taimaka wa jami'an tsaro wajen kiyaye aikata laifuka ta hanyar tona asirin bata gari da ke cikin al'umma.

A 'yan kwanakin nan ne dai aka gano wasu gidajen mari a garin Kaduna da Katsina inda ake zargin cewa ana azabtarwa da kuma cin zarafin mazauna wuraren da sunan basu tarbiyya.

Haka zalika an kuma kubutar da wasu yara da aka sace a Kano aka kai su Anambra inda har wasu daga cikin yaran harshensu ya sauya domin ko Hausa ba sa ji.

Sai dai bayan da shugaban Najeriyar ya fitar da wannan sanarwar, tuni mutane a shafukan sada zumunta suka fara mayar da martani inda wasu suke cewa shugaban ya ''makara'' wajen fitar da wannan sanarwa.

Wasu kuma sun jinjina wa gwamnatin sakamakon ta fito ta nuna rashin jin dadinta dangane da afkuwar wadannan lamrura.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Comrade Ibrahim cewa ya yi '' Alhamdulillahi, muna godiya kwarai Garba Shehu, mun gode duniya da lahira.''

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Sai kuma Haruna Musa cewa ya yi ''sanarwar nan ta zo a makare kuma mutanen Kano ba su jin dadin bambancin da ake nunawa wajen fitar da sanarwa idan wani abu ya faru a jihar.''

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Abubakar H Abdullahi cewa ya yi ya ji dadin jin wannan sakon.