An sake kai samame wani gidan Mari a Katsina

Rundunar 'yan-sandan Nijeriya a jihar Katsina ta ce jami'anta sun kai samame a wani gidan Mari a birnin Katsina, inda ake zargin an tsare mutane da dama.
Wannan shi ne gidan Mari na biyu da aka gano da kuma jami'an tsaro ke kai samame cikin kasa da mako guda a jihar Katsina.
Haka kuma makwannin baya-bayan nan dai an ceto daruruwan manya da yara-maza, daga wasu gidajen marin guda biyu, inda iyaye kan tura 'ya'yansu da fatan samun karatun Islamiyya da kuma gyara tarbiyyarsu, musamman ga kangararru.
To amma ana zargin daga bisani sukan tsinci kansu a kangin sarka da azabtarwa, da tsananin horo da rashin abinci da tsafta da kulawar lafiya, sai kuma zargin wa su ke yi na ana lalata da su.
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Gambo Isa, ya ce an gano gidan ne a unguwar Marusa, amma kangin da aka samu dauraru na gidan Mari a Marusa bai ka na wanda aka kubutar a garin Daura ba.
Gambo Isa ya shaidawa BBC cewa tuni wanda ya ke tafiyar da gidan ya tsere, to amma jami'an su sun baza koma dan gano inda ya ke tare da gudanar da bincike kafin daga bisani a mika su gaban kuliya.
Tun bayan gano gidan gwale-gwale da ke jihar Kaduna, shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin fara binciken irin gidajen, da cikakken bincike dan gurfanar da masu azabtar da yaran gaban shari'a.
Iyaye kan dauki 'ya'ya ko 'yan uwa da suka kangare su kai irin gidajen Marin da ake fakewa da gyara tarbiyya, da nufin za su zama mutanen kwarai. To amma labaran da ake samu ba mai dadi ba ne kan azabar da ake gana musu kama tun daga shugaban irin gidan har zuwa masu taimaka musu.











