Yadda ake azabtar da yara a cibiyar kangararru ta Kaduna

Bayanan bidiyo, Yadda a ke azabtar da yara a makarantar kangararru ta Kaduna

Latsa hoton da ke sama don kallon cikakken bidiyon

Daya daga cikin mutanen da aka ceto daga wata cibiya da hukumomi suka kira "wurin azabtarwa" a birnin Kaduna na Najeriya ya bayyana cewa rayuwa a gidan tamkar "zama a cikin wuta" ne.

"Idan kana yin sallah za su yi maka duka. In kana karatu ma su yi maka duka. Ko bacci ka ke idan za su tashe ka sai su yi maka bulala," in ji Isa Ibrahim, mai shekera 29, a hirarsa da BBC.

Tun farko dai rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar ta Kaduna ta ce mutanen da aka kubutar sun kai 300 zuwa 500 amma yanzu mutane 190 aka mika wa Ma'aikatar Ayyukan kyautata Rayuwar bil Adama da Zamantakewa ta jihar.