An sake kubutar da mutum 147 a gidan mari a Kaduna

Wani sanye da mari

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomi a jihar Kaduna da ke Najeriya sun ce sun kubutar da mutum kusan 150 a wani gidan mari da ake kira na Malam Nigga a Rigasa.

Gwamnan jihar Malam Nasir El Rufa'i ne ya jagoranci samamen tare da 'yan sanda a gidan marin a ranar Asabar.

Kwamishinar bunkasa rayuwar al'umma Hafsat Baba da ke cikin tawagar gwamnatin da ta kai sumamen ta ce daga cikin wadanda aka kubutar har da mata da yara wadanda aka yi zargin ana azabtar da su da nufin gyara hali.

Akwai mata 22 daga cikin 147 da aka samu kuma akwai yara guda hudu da wasu 'yan Kamaru biyu da 'yan Nijar guda biyu," in ji ta.

Sai dai ba ta yi karin bayani ba game da koshin lafiyar mutanen da aka samu, amma ta ce akwai wadanda likita ke diba lafiyarsu.

Gidan shi ne na uku da hukumomi suka ce sun gano kasa da wata guda a arewacin Najeriya.

Gidajen mari ko horo kamar yadda wasu suka fi daukarsu, iyaye ko 'yan uwa kan kai yaran da ake ganin yana neman kangarewa da nufin ladabtar da shi.

To amma labaran da ke fitowa daga wadannan gidajen ba masu dadi ba ne.