Ba abin da hukumar raya Neja Delta ta tsinana - Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau
Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da binciken kudi na kwakwaf kan ayyukan hukumar raya yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.
Shugaba Buhari ya ba da umarnin binciken ne tun daga shekarar 2001 har zuwa bana, lokacin da ya karbi bakuncin gwamnonin jihohin da ke karkashin ikon wannan hukuma a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun shugaban, Mallam Garba Shehu, ya ce za a binciki hukumar ne tun daga kafa ta tsawon shekara takwas saboda koke-koke da suka yi yawa game da ayyukanta.
Ya ce Buhari ya gaji da koke-koke da suka da ake yi game da hukumar wajen gazawarta na gudanar da ayyukanta da kuma yadda ake tafiyar da harakar kudaden na al'umma.
"Idan aka diba ayyukan hukumar a yankin mai arzikin fetir babu wani abin azo a gani da hukumar ta yi," in ji shi.
Ya kara da cewa Buhari yana son a gano inda kudaden hukumar ke shiga, bayan shekara biyu zuwa uku an kara yawan kudaden da ake ware wa hukumar a kasafin kudi.
Sai dai bai yi karin bayani ba game da kwamitin da zai gudanar da binciken da kuma lokacin da zai soma aiki.
Rahotanni sun ambato Buhari na cewa abin da ake gani yanzu haka a yankin Kudu maso kudu, bai yi daidai da dumbin dukiyar da aka rika warewa wannan hukuma ba.
An kafa hukumar raya yankin Neja Delta NDDC ne a shekarar 2008, zamanin mulkin marigayi Ummaru Musa Yar'Adua.
'Yan Najeriya da dama zargin wasu tsiraru ne ke bushasha da kudaden hukumar maimakon yankin da ke da arzikin man da tattalin arzikin Najeriya ke dogaro da shi.











