Barcelona ta karbe matsayin Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta doko Real Madrid daga saman tebur ta maye matsayin bayan da ta ci Eibar, 3-0 ita kuma Real ta sha kashi da ci 1-0 a gidan Real Mallorca.
Antoine Griezmann ne ya fara dora Barcelona a kan hanyarta ta cin wasa biyar a jere a dukkanin gasar da take, lokacin da ya daga ragar bakin a minti na 13.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci wasa ya fara mikawa a minti na 58 sai Lionel Messi ya kara jefa wa bakin ta biyu.
Minti takwas tsakani ne kuma sai shi ma Luis Suarez ya daga ragar Marko Dmitrovic da bal ya uku.
Tun kafin Messi ya ci ta biyun bayan an dawo daga hutu, Suarez din ya ci amma alkalin wasa ya ce ya yi satar gida.
Abokan hamayyar Barcelona Real Madrid sun yi asarar damarsu ta komawa saman tebur din bayan da mai masaukinsu Mallorca ta lika musu 1-0 a wasan na Asabar da daddare.

Asalin hoton, Getty Images
Rashin nasarar shi ne na farko da Real Madrid ta gamu da shi a gasar ta La Liga a bana.
Ita kuwa Mallorca nasarar ita ce ta farko da ta yi a gida a gasar a kan Real Madrid tun watan Fabrairu na 2006.
Haka kuma cin ya fitar da Mallorca wadda shekara biyu baya take a rukuni na uku na Sifaniya, daga matakin faduwa daga gasar ta La Liga, inda yanzu ta zama ta 14 a tebur da maki 10 a wasa tara da kuma bashin kwallo biyar.
Lago Junior shi ne ya ci bal din minti bakwai kacal da shiga fili, wadda ita ce ta farko da ya taba ci a La Liga, bayan da ya kwarara wa golan Madrid, Thibaut Courtois.
Real Madrid ba ta je Mallorca da karfi ba kasancewar 'yan wasanta Gareth Bale da Luka Modric da Toni Kroos dukkaninsu suna jinyar rauni.
Yayin da shi kuwa Eden Hazard ya tafi wajen murnar haihuwar da aka yi masa ta hudu, ranar Juma'a da dare.
Barcelona yanzu tana da maki 19 a wasa tara da bambancin kwallo 13, yayin da REal Madrid take da maki 18 da bambancin bal bakwai a wasannin tara.
Yanzu kungiyar ta Zidane za ta je Istanbul, babban birnin Turkiyya domin karawa da Galatasaray a gasar kofin Zakarun Turai, ranar Talata da dare.
A sauran wasannin na La Liga na mako na tara da aka yi ranar ta Asabar, Atletico Madrid a gidanta ta yi kunnen doki, 1-1 da Valencia, yayin da Getafe ta doke bakinta 'yan Leganés 2-0.











