Pogba ya gana da Zidane, matar Rakitic ta hana shi zuwa United

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba, mai shekara 26, ya gana da kocin Real Madrid, Zinedine Zidane a Dubai lokacin da suka je hutu, al'amarin da ya janyo hasashe dangane da makomar dan wasan na Faransa. (Mirror)

Kulob din Inter Milan na zawarcin dan wasan Manchester United na tsakiya dan asalin kasar Serbia, Nemanja Matic, mai shekara 31, is wanted by Inter Milan. (Sun)

Shi kuwa dan wasan tsakiya na Barcelona, Ivan Rakitic, mai shekara 31 ya fasa komawa Manchester United a watan Janairu kasancewar iyalansa ba sa son koma wa birnin Manchester. (Mail)

Kulob din na Manchester United ya nemi bayani dangane da lokacin da tsohon mai tsaron ragar Arsenal, Wojciech Szczesny, mai shekara 29 zai zama bai da yarjejeniya a kansa a lokacin bazara. (Goal)

Liverpool na yunkurin sayar da dan wasan tsakiya dan kasar Ingila, Adam Lallana, mai shekara 31, a karshen kakar wasanni. (Football Insider)

Wilfried Zaha na Crystal Palace mai shekara 26, ya sadaukar da kaso 10 na albashinsa ga ayyukan alkairi a kasarsa, Ivory Coast da suka hada da gidan marayu da 'yar uwarsa take gudanarwa.(Mirror)