Kada ku kyamaci Musulmi - Macron

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi gargadi a kan "nuna kyama" a kan musulmi ko hada addinin Musulunci da yaki da ta'addanci.
"Ya kamata mu hada kai da duka 'yan kasa" a cewar Shugaba Macron lokacin da ya yi jawabi ga 'yan jarida tare da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a ranar Laraba.
Wannan ya zo ne a lokacin da matar ta ce za ta kai dan siyasar mai tsattsauran ra'ayi kotu bayan da ya yi Allah-wadai da ita don ta sanya hijabi a cikin mutane.
Faransa na da kimanin Musulmi miliyan biyar a kasar.
Ita ce kasar da ta fi kowace yawan musulmi a yammacin nahiyar Turai.
Faransa kasa ce wadda ke raba siyasa da addini, sanya hijabi na cikin manyan abubuwan da suka kawo ce-ce-ku-ce a 'yan shekarun nan.
A makon da ya gabata wata uwa musulma wadda ta sanya hijabi a wata tafiya da makarantar danta ta shirya zuwa majalisar yankin Bourgogne da ke a gabashin Faransa inda wani ya zage ta.
A ranar Laraba Shugaba Macron ya nemi a fahimci addinin musulunci kuma ya yi Allah-wadai da abin da ya kira "mummunan ratse" na hada musulunci da ta'addanci
"Akwai ganganci sosai ga masu tsokacin siyasa" a cewarsa. Ya kara da cewa "tarayya ba ta'addanci ba ne."











