United na da halin bunkasa kungiyar— Solskjaer

Asalin hoton, Getty Images
Ole Gunnar Solskjaer ya ce Manchester United tana da sarari da kudin da za ta karfafa kungiyar a wasannin bana.
United tana ta 12 a kasan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da 'yan ukun karshe, kuma Liverpool ta daya ta bai wa United tazarar maki 15.
Ranar Lahadi ne Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na tara a gasar cin kofin Premier da za su fafata a bana.
Mahukuntan Manchester United United na shan suka kan kasa taka rawar gani da kungiyar ke yi a wasannin Premier bana.
United ta kashe fan miliyan 145 wajen sayo Harry Maguire da Aaron Wan Bissaka da kuma Daniel James, kuma Solskjaer ya ce akwai kudi a kasa da zai karo wasu a Janairu.
Solskjaer ya c e akwai jan aiki a gaban United na takawa Liverpool burki a shirin da take na lashe kofin Premier bana wanda rabonta da shi tun 1990.
Kocin ya kara da cewar kwantiragin shekara uku ya sa hannu a Old Trafford, saboda haka suna da shiri na dawo da martabar kungiyar a fanni tamaula.







