Shugaban Turkiyya Erdogan 'ya jefa wasikar Trump a kwandon shara'

Turkish President Recep Tayyip Erdogan. Photo: 13 October 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A wasikar an cewa Shugaba Erdogan: "Kar ka zama wawa!"
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jefa wasikar Shugaba Donald Trump "cikin kwandon shara", kamar yadda aka shaida wa BBC.

A cikin wasikar da aka rubuta ranar 9 ga watan Oktoba aka kuma aika ta bayan da aka janye dakarun Amurka daga Syria, Mista Trump ya shaida wa Mista Erdogan cewa "Kar ka zama mai taurin kai! Kar ka zama wawa!"

Majiyoyi daga fadar gwamnatin Turkiyya sun shaida wa BBC cewa Mista Erdogan "bai ko duba wasikar ba."

A ranar da wasikar ta isa, a ranar ne Turkiyya ta kaddamar da wasu hare-hare kan dakarun Kurdawa ta kan iyaka.

Trump's letter to Erdogan

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Trump ya shaida wa Mr Erdogan cewa: 'Ka zo mu kulla yarjejeniya!'
Presentational white space

Shugaba Trump ya fuskanci suka sosai kan janye dakarun, inda masu suka suka ce hakan ne ya bai wa Turkiyya damar kai hare-haren soji.

Yawanci sukar ta fito ne daga jam'iyyar Mista Trump.

A wani lamari da ba a saba gani ba, 'yan majalisar dokoki 129 na jam'iyyar Trump ta Republican sun hade kai da 'yan Democrat wajen yin Allah-wadai da matakin a ranar Laraba.

Kakakin majalisar dokoki Nancy Pelosi ta yi wata ganawa da Shugaba Trump kan batun, wanda hakan ya jawo suka fice daga dakin ganawar ita da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa Charles Schumer.

Shugabannin jam'iyyar Republican sun ce halayyar da Ms Pelosi ta nuna "ba ta dace ba", sun kuma yi Allah-wadai da ficewar da ta yi daga dakin taron.

Ms Pelosi da Mista trump sun kuma zargi juna da rushe al'amura, inda shugaban daga bisani ya wallafa wani hoto a Twitter na yadda suke sa-in-sar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

Presentational white space

Amma 'yan jam'iyyar Democrat sun yi ta yabon yanayin hoton, suna cewa ta kafa tarihi a hoton kuma ya nuna kyakkyawan yanayi na Ms Pelosi.

Ms Pelosi ta mayar da hoton ya kasance a gaban shafinta na Twitter.

Tun da farko a ranar Laraba, Shugaba Trunp ya ce Amurka ba za ta shiga tsakanin ba a hare-haren da Turkiyya ke kai wa Syria saboda "ba a kan iyakarmu suke ba", ya kuma kira tsofaffin abokan Amurkan Kurdawa da "ba mala'iku ba."

Karin labarai masu alaka