Rasha za ta shiga tsakanin Turkiyya da Syria
Rasha ta ce ba za ta bari yaki ya kaure tsakanin Turkiyya da Syria ba, yayin da Turkiyyar ke ci gaba da kai hare-hare kan mayakan kurdawa a arewacin Syria.
A cewar wakilin Rasha na musamman a Syria Alexander Lavrentyev, Rasha ba za ta taba bari yaki ya barke a tsakanin kasashen biyu ba.
Masu suka sun ce janye sojojin da Amurka ta yi ne ya ba wa Turkiyya damar cin karenta ba babbaka a yankin.
Rasha na daga cikin manyan kawayen Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad.
A ziyarar da ya kai Hadaddiyar Daular Larabawa, Mr Lavrentyev ya bayyana cewa Rasha ba za ta aminta da hare-haren da Turkiyya ke kai wa ba.
Ya kara da cewa jami'an Turkiyya da na Rasha na kan tattaunawa kan lamarin.
Dakarun Rasha da aka girke a Syria tun a shekarar 2015 har yanzu na rangadi a yankin.
Abunda ya faru kafin yanzu
Makon da ya gabata ne Turkiyya ta kaddamar da hare-hare a arewacin Syria da nufin kawar da mayakan kurdawa da ake kira SDF daga yankin.
Dama Turkiyya na yi wa mayakan kallon 'yan ta'adda.
Hakama gwamnatin Turkiyyar na son samar da sansani a yankin da nufin maido da 'yan Syria da a yanzu ke gudun hijira a kasar.
To sai dai masu suka na zargin cewa wadanda Turkiyya ke kai wa harin fararen hula ne, inda suka yi gargadin cewa Turkiyya na kokarin aikata kisan kiyashi ne.

Asalin hoton, Getty Images
Alkaluman da majalisar dinkin duniya ta fitar sun nuna cewa an kashe gwamman fararen hula, kuma mutane 160,000 sun tsere daga muhallansu.
A baya mayakan Kurdawa sun hada hannu da sojojin Amurka wurin fatattakar kungiyar IS daga Syria.
A yanzu kuma sun bayyana janye sojojin Amurka da shugaba Trump ya yi a matsayin yaudara.
Ana fargabar rikicin zai iya sanadiyyar sake bullar kungiyar IS a Syria.
Yanzu haka ana tsare da dubbai daga cikin tubabbun mayakan kungiyar ta IS da iyalansu, kuma wasu rahotanni na cewa fadan ya yi sanadiyyar tserewar wasu daga cikinsu.
Haka ma kungiyoyin agaji da dama sun dakatar da ayyukansu a yankin tare da kwashe ma'aikatansu.
Yayin da matsin lamba ya yi kamari, mayakan Kurdawa sun bayyana kulla yarjejeniyar hada-hannu da gwamnatin Syria wurin mayar wa Turkiyya martani.
A cewar shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan,Turkiyya za ta ci gaba da kai hare-hare har sai ta cimma burinta a yankin.

Asalin hoton, AFP
Wane irin takunkumi ne Amurka ta kakabawa Turkiyya?
Amurka ta sanar da saka takunkumi kan kadarorin ma'aikatun tsaro da makamashi da kuma harkokin cikin gida na Turkiyya, bayan matsin lamba kan gwamnatin Amurka daga 'yan majalisa.
Bugu da kari, Mr Trump ya sanar da karin haraji da kashi 50 tare da dakatar da yarjejeniyar dala biliyan 100 da gwamnatinsa ke kan kullawa da Turkiyya.
Mr Trump ya kuma rubuta a shafinsa na Twittwe cewa ''Amurka da kawayenta sun kubutar da Syria daga kungiyar IS kuma ba za su sa ido Turkiyya ta ruguza wannan nasarar ba''
Shi ma mataimakinsa Mike Pence ya ja kunnen Turkiyya da ta kwana da sanin cewa akwai karin takunkumai, idan har ba ta gaggauta tsagaita wuta ba tare da tattauna hanyar samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Asalin hoton, Getty Images












