Fadan Turkiyya da Siriya 'ba matsalarmu ba ce' - Trump

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ''ba matsalarmu ba ce'' idan Turkiyya ta shiga Siriya. Trump ya kuma ce abokan kawancen Amurka wato Kurdawa ''ba Mala'iku ba ne.''
Amurka na fuskantar Alla-wadai bayan ta janye sojojinta daga Siriya inda wasu ke cewa hakan ya ba wa Turkiyya damar ketara iyaka ta far wa mayakan Kurdawa.
Shugaban Amurka ya shaida wa manema labarai a fadarsa cewa Amurka ba '''yar sanda ba ce''.
"Lokaci ya yi da za mu koma gida," a cewarsa.
Turkiyya ta far wa arewacin Siriya a mako da ya wuce inda ta kori mayakan Kurdawa daga kusa da iyakarta wadanda ake kira da ''People's Protection Units (YPG), domin ta kafa "tsararren wuri" a kusa da iyakarta domin ta ba wa 'yan gudun hijira daga Siriya kimanin miliyan biyu damar zama a can.

Aikin na Turkiyya ya zo ne bayan da Trump ya bayar da umurni ga dakarun Amurka su bar tekun da ke a wurin.
Mayakan na Kurdawa sun taka rawa sosai inda suka yi kawance da Amurka wajen murkushe mayakan IS. Ana fargabar kokar Kurdawa daga wurin zai iya dawo da mayakn IS.

Asalin hoton, others
Shugaba Trump ya ce yana ganin abin da ke faruwa a kan iyakar Turkiyya da Siriya a matsayin wani "tunani mai kyau" ga Amurka.
"Sojojinmu sun fita daga wurin. Dakarunmu na nan cikin koshin lafiya. Suna da aikin da za su yi. Za su iya yin sa ba tare da sun yi yaki ba" a cewarsa.











