Ko kun san yadda kananan yara ke bata a Kano?

Asalin hoton, Getty Images
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, bayanai sun fito da ke nuna cewa akwai gomman yara da suka bata a wasu yankunan jihar, wadanda kuma ake zargin sace su aka yi tun daga shekarar 2014.
Wasu iyaye sun ce an sace masu yaransu kuma har sun kafa kungiya don fafutukar gano inda 'ya'yansu suke.
Ko a makon da ya gabata, rundunar 'yan sandan jihar ta gano wasu yara tara da aka sace daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya inda aka sayar da su a jihar Anambra da ke kudancin kasar.
An gano cewa an sauya wa wadannan yara suna da addini bayan da aka sace su.
Rundunar ta kama wasu mutum shida da zargin sayar da yaran.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama a jihar Kano sun lashi takobin bin kadin wannan batu na zargin satar yara daga jihar da yadda ake sauya musu sunaye tare da sayar da su ga ma'auratan da ke bukatar 'ya'ya.
Iyayen da suka ce an sace masu yaransu, sun kafa wata kungiya ta fautukar ganin an karbo musu yaransu kuma sun shaida wa BBC cewar sun rasa yara sama da arba'in.
Iyayen sun ce a kullum suna cikin zulumin halin da 'ya'yan nasu ke ciki.
Sakataren kungiyar, Shu'aibu Ibrahim Tajidi wanda kuma aka sace dansa Ayatullahi mai shekara 3 da suka gabata, ya ce "A kan dandamalin kofar gida yana wasa da 'yan uwansa aka sace shi.
"Na shiga damuwa, na shiga dimuwa saboda tashin hankalin da na shiga shi ne, duk a cikin 'ya'yana da shi na fi shakuwa."

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar iyayen yaran sun shafe kimanin shekara uku suna fautukar ganin an nemo masu yaransu da aka sace.
Da yawa daga cikinsu sun ce sun fara fitar da rai da sake ganin 'ya'yansu.
Wata mahaifiya da aka sace 'yarta mai shekaru biyu da rabi, Hajiya Zainab Abdullahi Giginyu ta shaida wa BBC cewa ba ta fitar da rai ba don "kullum muradina ban ki a ce gata ba."
Ta ce an sace 'yar ne a gidansu bayan "ta ci abincin rana ko hannu ban wanke mata ba. Na tashi zan wanke mata hannu na neme ta na rasa ko sama ko kasa.
"Na leka waje in gani ko fita ta yi, ko yara sun yi gaba da ita aka dudduba ba a ganta ba har yau.


Asalin hoton, Getty Images
Tun bayan da rudunar 'yan sanda ta sanar da gano wasu yara tara da aka sace aka siyar da su a jihar Anambra wadannan iayaye suka fara sa ran za a gano nasu yaran.
Manyan kungiyoyin kare dan Adam a jihar sun dauki alwashin tabbatar da an share wa iyayen yaran hawaye, ta hanyar zaburar da gwamnati ta kara kaimi wajen ganin an ceto yaran nasu.
Ibrahim Wayya, shugaban Zauren Kungiyoyin kare fararen hula a Kano ya ce "muna kira ga gwamnatin jihar Kano ta duba ta ga irin tagomashi da taimako da za ta iya bai wa iyayen wadannan yaran."
Rahotanni dai sun bayyana cewa kimanin yara 47 ne suka bata a jihar.
A watan Fabrairun shekarar 2017, daruruwan iyaye mata da aka sace 'ya'yansu a jihar Kano suka gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai kan yadda gwamnatin jihar Kano ke nuna halin ko in kula kan batun satar yara.
Tuni dai wata kungiyar dattawa masu kishin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa ta koka kan satar yara da ake yi a jihar ana kai su kudancin kasar.
Kungiyar ta bayyana ra'ayinta kan wannan batu ne ta bakin mataimakin shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar Mallam Ibrahim Ado Kurawa.
A hirarsa da BBC Hausa, Ado Kurawan ya ce akwai bukatar gwamnatin jihar Kano ta hada kai da ta jihar Anambra don nemo sauran yaran da su ma iyayensu ke kukan bacewarsu lokaci mai tsayi ba a gansu ba har yanzu.
Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar BBC da Ado Kurawa:












