Tsohon jakadan Najeriya ya ce Buhari ya yi gaggawar zuwa Afirka ta kudu

Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto, Muhammadu Buhari Shugaban Najeriya

Wani tsohon jakadan Najeriya da yakan yi sharhi kan harkokin diflomasiyya, Ambasada Suleiman Dahiru, ya ce ziyarar da Shugaba Muhammadu Buhari zai kai kasar Afirka ta kudu domin ganawa da takwaransa, Cyril Ramaphosa, ba ta dace ba a yanzu, inda ya ce ziyarar ta yi kusa-kusa ganin yadda a kwanan nan ne aka kai hare-haren kin jinin baki, ciki har da 'yan Najeriya a kasar.

Jakada Suleiman Dahiru ya ce bai ga laifin Shugaba Buhari wajen amsa gayyatar da Afirka ta kudu ta yi masa ba sai dai a cewar shi, akwai bukatar a ce ziyarar ta zo ne a lokacin da 'yan Najeriyar suka huce game da kashe-kashen da aka yi wa 'yan kasar a Afirka ta kudun, da kuma bannata dukiyarsu.

Sai dai jakadan ya ce kamata ya yi ziyarar ta zama silar kawo karshen abubuwan rashin jin dadi da suka faru tsakanin Najeriya da Afirka ta kudu da biyan mutanen da hare-haren suka shafa diyya ta hanyar samar da doka da za ta tabbatar da hakan.

Masu kai hare-hare kan baki a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Ya ce ya kamata jagororin biyu su yi tattaunawa cikin tsanaki domin lalubo bakin zaren matsalar da ke neman wuce gona da iri da nufin gyara dangantakar da ta yi tsami tsakanin kasashensu da nuna kin amincewa da kisan kiyashin da ake yi wa 'yan Najeriya ko sace musu dukiyoyinsu.

A ranar Laraba ne shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari zai fara ziyarar a kasar Afirka ta kudu tsawon wuni uku, bayan dambarwar da aka yi ta yi sakamakon hare-haren da aka kai kan baki 'yan kasashen waje.

Shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ne ya aika wa Buhari goron gayyata

Shugaba Buhari zai kai ziyarar ne sakamakon goron gayyata da Shugaba Cyril Ramaphosa ya aika masa tun bayan jerin hare-haren da komawar 'yan Najeriya gida daga Afirka ta Kudu.

Tun da farko, cikin wata sanarwa, mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce jagororin biyu za su tattauna batutuwa ne da suka shafi walwalar 'yan Najeriya.

A hukumance gwamnatin Afirka ta Kudu ta nemi afuwar Najeriya kan tashin hankalin da ya faru.

Najeriya da Afirka ta Kudu su ne manyan kasashe mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka.