Yadda jami'an kwastam suka lakada wa dan jarida duka

Lamine
Bayanan hoto, Dan jaridar ya ce jami'an sun yi masa duka har da keta riga

Wani dan jaridar gidan rediyon Express da ke birnin Kano, Lamin Hassan ya dandana kudarsa a hannun jami'an fasakauri a lokacin da yake aiki.

Dan jaridar dai ya shaida wa BBC cewa ya samu rahoto kan irin yadda jami'an hukumar ta fasakauri ke far wa masu sana'ar sayar da ruwan zam-zam da dabino a unguwar Gwammaja da ke birnin, shi ya sa ya tashi ya tafi domin yin rahoto a kai.

Ya ce ya nuna wa jami'an shaidar da ke nuna shi danjarida ne amma suka yi burus suka hana shi aikinsa.

Bayan nan ne kuma suka bi bayansa inda suka lakada masa duka tare da kwace masa abun daukar magana da fasa masa waya sakamakon duka da kan bindiga.

To sai dai hukumar Hana fasa kaurin mai kula da shiyar Kano da Jigawa ta bakin mai magana da yawunta, ASP Isa Danbaba ta ce sun sami labarin abun da ya faru, Kuma suna bincike kan al'amarin sannan za su hukunta jami'an nasu da ke da hannu wajen wannan aiki.

Danbaba ya kara da cewa dukkan jami'an nasu da dan jaridar sun yi kuskure

Amma ya ce wasu daga cikin jami'an gidan radion na Express Abdullahi Isa da shi dan jaridar da aka lakada wa duka, Lamin Hassan sun zauna da juna domin sasantawa.

To sai dai hukumar gudanarwar gidan rediyon Express Radio ta bakin Shugaban gidanta, Ali Baba Kusa ta ce ko duk da sun zauna da hukumar Hana fasa kaurin ba za su hakura ba saboda dukan da suka yi wa ma'aikacin nasu.

Ya kuma kara da cewa sai da suka kai dan jaridar asibiti domin samun kulawa ta gaggawa saboda irin dukan da aka yi masa, inda ya ce suna gana wa da lauyoyinsu kuma da zarar sun kammala shawara da su za su sanar da matakin da za su dauka nan gaba.