Jose Mourinho: 'Eto'o ya cancanci ya lashe Ballon d'Or'

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Man United da Chelsea da Real Madrid, Jose Mourinho, ya yi imanin cewa tsohon tauraron dan wasan Kamaru Samuel Eto'o ya cancanci ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya ko da sau daya ne.
A kwanan nan ne tsohon dan wasan Barcelona da Real Madrid da Inter Milan da Mallorca, mai shekara 38, ya yi ritaya daga taka-leda.
A tsawon shekara 22 da ya yi yana wasa, Eto'o ya lashe kofin Kasashen Afirka sau biyu da kuma Champions League guda uku.
Mourinho ya hadu da Eto'o ne a karon farko a Inter Milan a kakar 2009-2010, inda suka lashe dukkanin kofunan da Inter Milan ta buga a shekarar - Serie A da Italian Cup da kuma Champions League.
Sai kuma suka sake haduwa a Chelsea shekara uku bayan haka na dan wani lokaci.
"Abin mamaki ne in ka tuno cewa Samuel Eto'o bai taba lashe Ballon d'Or ba duk da irin bajintar da ya yi a harkar wasansa," Mourinho ya fada wa wani gidan rediyon kasar Kamaru.
"Eto'o ya taka wa manyan kungiyoyin duniya leda. Ya ci kwallaye da dama kuma ya samu nasarori a lig daban-daban.
"Ya buga wasannin karshe har sau uku na Champions League, guda biyu da Barcelona kuma ya ci kwallo a kowanne. Sannan ya lashe kofin a Inter Milan da sauran lig lig da ya lashe.
"Shi ne dan wasan gaba mafi kyau a duniya tsawon shekaru, saboda haka ina ganin ya dace ya lashe Ballon d'Or. Sai dai ba yadda muka iya."
Samuel Eto'o ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka sau hudu, yayin da kuma ya zama na uku a kyautar Fifa World Player a 2005, wadda aka daina bayarwa a yanzu - bayan Ronaldinho da Frank Lampard.

Asalin hoton, Getty Images
Ya murza-leda a kungiyoyi 13 a kasashe shida kuma ya ci wa kasarsa ta Kamaru kwallo 56 a wasa 118.
A ranar 7 ga watan Satumbar nan ne kuma ya jingine takalmansa, inda ya ce zai tafi hutu domin zama da iyalinsa da kuma tsara yadda rayuwarsa za ta kasance.











