'Har abada ba zan sake komawa Afirka ta Kudu ba'

Bayanan bidiyo, Ni da Afirka ta Kudu har abada

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Tawagar 'yan Najeriyar da suka tsere wa hare-haren kin jinin baki daga Afirka Ta Kudu sun isa birnin Legas da daren Laraba.

Tawagar mai kunshe da mutum 314 ita ce ta biyu da ta isa birnin na Legas.

Daya daga cikin wadanda rikicin ya shafa ya bayyana wa BBC cewa ya rasa komai da yake da shi a rikicin.