Yadda na tsallake rijiya da baya a gobarar da ta kashe almajirai 27

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Malamin da ke kula da makarantar al'kur'anin nan da wuta ta kashe almajirai 27 ya shaida wa BBC yadda Allah ya tseratar da shi.
Mohammed Lamine Barry ya ce shi da daliban suna tsaka da bacci a daren Talata lokacin da gobarar ta tashi a dakin kwanan yaran a makarantar koyon karatun al'kur'anin da ke Paynesville kusa da babban birnin Monrovia.
Ya ce ya farka cikin dare sai dai a lokacin aikin gama ya gama ta yadda wutar ta mamaye ko ina na gidan. A cewar malamin.
Ya tsere da mai dakinsa da yaronsa amma a cewar shi, gobara tana ci a daya bangaren ginin kuma duka yaran sun bar wajen.
Wasu daga cikin yaran shekarunsu bai wuce 10 gama. In ji malamin.
Malamin makarantar ya kara da cewa kofofin dakin kwanan ba a rufe suke ba.
Kofofin a bude suke sai dai kawai wutar ta ci karfin kowa yayin da mutane suke cikin bacci. Yace hayakin da ya rika tashi ne ya kashe mutane kafin ma wutar ta isa inda suke.
"A lokacin da na ziyarci makarantar da safiyar ranar Alhamis, masu bincike tuni sun isa wajen domin fara duba abinda ya ja ta'asar, kamar yadda malamin ya shaida".
Kakakin rundunar 'yan sanda ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akwai yiyuwar tartsatsin wuta ne ya jawo hadarin gobarar sai dai jami'in ya ki ya fadi ko tashin gobarar wani hari ne da aka kai.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai gobarar ta tashi inda ta kashe akalla mutum 27 a makarantar Alkur'anin, inda kuma ake kyautata zaton wutar ta tashi ne da tsakar dare a dakin kwanan daliban.
Shugaba George Weah ya bayyana alhininsa a sadda ya ziyarci makarantar, inda ya mika ta'aziyyara ga iyalan mamatan.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kakakin 'yan sandan, Moses Carter ya ce matsalar lantarki ce ta haddasa gobarar, amma ana ci gaba da bincike, kamar yadda ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani shaidan gani da ido, Fasto Emmanuel Herbert ya shaida wa BBC cewa karar wutar ce ta tashe shi daga bacci, inda daga nan ya yi kururuwar neman a kawo agaji.
"Da na duba ta taga, sai na ga gaba daya wurin na ci da wuta."
Amma ya ce bai iya shiga cikin ginin ba saboda mashiga daya da ginin ke da shi na rufe a lokacin.
Yawancin 'yaran da gobar ta rutsa da su 'yan shekara 10 zuwa sama ne, kamar yadda jami'ai suka shaida wa AFP.
Daruruwan mutane sun taru a wajen makarantar
Daga Jonathan Paye-Layleh, a birnin Paynesville, Laberiya

Daruruwan mutane sun taru inda suke bayyana mamakinsu yayin da motar agaji ta kungiyar Red Cross ke daukar gawarwakin daliban daga dakin kwanansu a birnin Paynesville, mai nisan kilomita 11.3 daga Monrovia.
Jama'a na cike da alhini
Cincirindon mutane sun taru domin gane wa idanunsu abin da ya faru.
Da kyar 'yan sanda ke iya kawar da mutanen domin motar agajin ta samu hanyar wucewa.
Shugaban kasar, George Weah na daga cikin wadanda suka ziyarci makarantar, kuma ana sa ran zai halarci jana'izar a Monrovia.
An shirya gudanar da jana'izar mamatan ne a ranar da aka gobarar ta faru bisa tsarin addinin Islama.
Karin jama'a na ci gaba da yin tururuwa domin zuwa makarantar da gobarar ta faru domin gane wa idanunsu.











