'Yan majalisa za su je kotu domin taka wa Boris Burki

PA Media

Asalin hoton, PA Media

'Yan majalisar dokokin Birtaniya har da wadanda aka kora daga jam'iyya mai mulki na shirin shigar da kara gaban kotu ko da kuwa Firai Ministan kasar ya ki amince wa da jinkirta ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Ana sa ran sarauniya za ta amince da wani kudiri da zai bukaci firai ministan kasar, Boris Johnson ya nemi a kara jinkirta ficewar kasar daga Tarayyar Turai a 31 ga watan Oktoba domin guje wa kasar ta fita ba tare da yarjejeniya ba.

Sai dai a nasa bangaren Mista Johnson ya bayyana cewa gwara ya mutu cikin magudanar ruwa kan ya bukaci jinkiri na ficewar kasar.

A yanzu haka dai 'yan majalisar sun kafa wani kwamiti na musamman na shari'a da za su je kotu domin kalubalantar kudirin firai ministan.

Kudirin wanda jam'iyyu daban-daban suka amince da shi a ranar Juma'a, ya bukaci firai ministan ya kara tsawaita wa'adin da ya sa na ficewar kasar zuwa watan Janairun 2020.

To sai dai hakan zai yi aiki ne kawai idan har an samu amincewa tsakanin majalisar dokoki da kuma Tarayyar Turai na ficewar kasar tare da yarjejeniya.

Duk da cewa gwamnatin ta bayyana cewa za ta bi tsarin doka, Mista Johnson ya bayyana hakan a matsayin tilasta masa ya rubuta wa Tarayyar Turai takarda kan jinkiri wanda bai da amfani.

Ofishin firai ministan ya bayyana cewa 'yan Birtaniya sun fito fili sun bayyana cewa suna son ficewar Birtaniyar daga Tarayyar Turai.

A makon nan ne dai 'yan jam'iyyar Conservative mai mulkin Birtaniyar da na bangaren hamayya suka kayar da gwamnatin kasar a mataki na farko na kokarin da suke yi na hana ta ficewa daga Tarayyar Turai.

Majalisar ta gudanar da zabe inda ta karbe ikon gudanarwa daga masu goyon bayan firai ministan da kuri'u 328, inda ya sami 301.

Wannan ne ya ja har aka gabatar da kudurin doka da zai jinkirta ranar ficewar Birtaniya daga Tarayyar ta Turai.