'Yan jarida nawa aka kashe a bara?

- Marubuci, Daga Reality Check team
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Kungiyar 'yan Jarida ta duniya, IFJ ta ce akalla 'yan jarida 95 aka kashe a bara a lokacin da suke gudanar da ayyukansu.
Alkaluman ya zarce na shekara ta 2015, sai dai bai kai na shekarun baya ba lokacin da ake tsananin rikici a Iraqi da Syria.
A shekara ta 2006 aka samu alkaluma mafi yawa inda aka kashe 'yar jarida 155.
Kididdigar ta hada da duk wani wanda ke aiki a wata kafar yada labarai.
Kisan da ya fi jan hankali a shekara ta 2018, shi ne wanda aka yi wa fitaccen dan jaridar nan na Saudiyya, Jamal Khashoggi.
A watan Oktoban bara aka kashe shi lokacin da ya je ofishin jakadancin Saudiyya da ke Turkiyya.

Asalin hoton, Getty Images
Kisan Khashoggi ya janyo rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, sannan kasahsen duniya da dama sun ta alla-wadai.
A watan jiya a Burtaniya, wata 'yar jarida Lyra McKee ta mutu a kan titin Londonderry lokacin da take daukan rahoton wata zanga-zangar da ta barke.
Jami'an tsaro Arewacin Ireland sun dauki alhakin kisan yan jaridan.

Ina ne mafi hadari?
Har yanzu Afghanistan na daya daga cikin kasashen mafi hadari ga 'yan jarida, mutum 16 suka mutu a cikin shekarar da ta gabata.
'Yan jaridar Afghanistan tara aka kashe a rana guda a birnin Kabul, lokacin da suka isa wani wurin da aka kai harin bam domin daukan rahoto.
Wani mutum da ya yi basaja a matsayin dan jarida ne ya tada bam din da ke jikinsa.
A gabashin Afghanistan kuma, an kashe wakilin BBC Ahmad Shah a wani jerin hare-haren da aka kai lardin Khost.
An kuma kashe 'yan jarida da dama a bara a Amurka.
An harbe mutum biyar a wani harin da aka kai kan cibiyar jaridar Gazetta da ke Maryland, wanda ake zargin wani mutum da ya yi kokarin kai karar jaridar shekara da shekaru da ya kai harin.
Karuwar rashin hakuri, siyasa da aikata laifuka da kuma cin hanci da rashawa su ne manyan abubuwan da ke janyo wadanan mace-macen, a cewar IFJ.
Wannan na bada gudunmawa wajen kisan 'yan jarida a yankunan, birane da jihohin da suke aiki.
A kowanne farkon watan Disamba Kungiyar Kare hakkin 'yan jarida ta CPJ na daukan hoton 'yan jarida da ke gidan yari.
Alkaluman ya kunshi duk wanda ke aiki a matsayin dan jarida, wadanda aka garkame a gidan yari kan dalilan da ke da alaka da aikinsu.
Kasashen da ke da mafi yawan 'yan jarida a gidan yari a 2018:
- Turkiyya 68
- China 47
- Masar 25
- Saudiyya da Eritrea 16
'Yan jaraida da demokradiyya
Majalisar dinkin duniya za ta sa ido a shekarar nan kan 'yancin jarida a fannin demokradiyya, musamman ma a lokutan siyasa.
A wata sanarwa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ''demokradiyya ba ta cika ba muddin ba a samar da hanyoyin samun cikakkun bayanai na gaskiya da sahihanci.''

Asalin hoton, Getty Images
Wata mamba a kungiyar karen 'yancin 'yan jarida ta CPJ, Courtney Radsch ta ce rashin bai wa 'yan jarida cikakkiyar 'yanci na faruwa a kasashe da dama, musamman ma a Phillipenes da kuma Amurka.
Ta na da yardar cewa kafofin sada zumunta da kuma kafar intanet na daya daga cikin abubuwan da ke kara tunzura lamarin.
''Cin zarafi ta kafar intanet da kuma yi wan 'yan jarida barazana, musamman ma mata su na kara tunzura mumunar yanayin da ake shiga.''
A wata zaman tattaunawar da za ta yi kan 'yancin 'yan jarida a wannan shekarar, kungiyar Reporters withouth Borders (RSF) ta ce ta dauki lamarin a matsayin babban matsala.
''Ba a taba samun lokacin da ake yawaita aika wa 'yan jaridan Amurka sakonnin barazana ba, wadanda ke janyo su nemi tsaro daga kamfanonin tsaro masu zaman kansu.''
Amurka ta koma kasa a jadawalin kasashen da RSF ke fitar wa wadanda ke bada 'yancin ga 'yan jarida a wannan shekarar, tare da Indiya da kuma Brazil.
Kuniyar ta kuma kara da cewa, kasashe biyu da ake take 'yancin 'yan jarida da ya fi na Amurka kazancewa akwai Venezuela, Rasha da kuma China.











