An kashe mutum daya a wani harbi a Amurka

A San Diego County Sheriff's Deputy secures the scene of a shooting incident at the Congregation Chabad synagogue in Poway, north of San Diego, California, U.S. April 27, 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun yi saurin tare hanyoyin shiga wurin da harin ya auku a Poway

Wani dan bindiga ya bude wuta a wani wurin ibadar yahudawa a jihar California, inda ya kashe wata mata da kuma raunta mutum uku.

An kama wani mai shekarar 19 bayan harin a Poway dake arewacin birnin San Diego.

Rahotanni sun bayyana cewa ana wani bikin Yahudanci ne a lokacin da harbin ya auku.

'Yan sanda ba su bayyana dalilin kai harin ba amma Shugaban Amurka Donald Trump ya ce harin ya yi kama da na kin jini.

Harin dai na zuwa ne watanni shida bayan da wani dan bindigar ya kashe mutum 11 a wani wurin ibadar yahudawa a Pittsburgh, wanda kuma shi ne harin nuna kin jinin yahudawa mafi muni a tarihin Amurka.

Shugaban 'yan sanda na lardin San Diego Bill Gore ya shaida wa 'yan jarida cewa masu bincike na bitar shafukan sada zumuntar wanda ake zargi da kai harin da kuma wata budaddiyar wasika da aka buga a intanet.

"A lokacin harin, mutum hudu sun samu raunuka kuma an kai su asibitin Palomar," a cewarsa. "Daya ta ce ga garinku na. Sauran ukun na asibiti inda ake ba su kulawa."

San Diego Police secure the scene of a shooting incident at the Congregation Chabad synagogue in Poway, north of San Diego, California, U.S. April 27, 2019

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ana wani bukin yahudanci ne a lokacin da harin ya auku

Magajin garin Steve Vaus ya ce an harbi limamin wurin bautar a hannu.

Shugaban 'yn sanda Mista Gore ya ce an kira 'yan sanda wurin bautar na Chabad kafin karfe 11.30 wato karfe 6.30 agogon GMt bayan da mutumin ya bude wuta d bindiga kirar "AR-15".

Wani dan sanda ya yi kokarin harbin dan bindigar amma bai same shi ba.

Daga baya ne dai aka kama dan bindigar.

San Diego Sheriff deputies look over the Chabad of Poway Synagogue after a shooting on Saturday, April 27, 2019 in Poway, California

Asalin hoton, AFP