Dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 18 a kwaleji

This photo shows the Kerch bridge, with some cranes along its edges, in daylight

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan gadar ce ta hada zirin Kerch da yankin Crimea

Shugaban yankin Crimea Sergei Aksyonov ya ayyana zaman makokin kwanaki uku bayan harin bindiga da na bam da aka kai wata maranta ta ke birnin Kerch da kuma mutane 19 suka mutu.

Gwammai da na kwance a gadon asibiti wasu cikin mawuyacin hali. Masu bincike na Rasha sun ce harin na kunar bakin wake ne da wani dalibi mai shekara 18 Vladislav Roslyakov ya tashi bam din da ke jikinsa a tsakiyar makarantar.

Rahotanni sun ce ya dasa wani bam din a kantin saida kwalam da makulashe a kwalejin, kafin ya fito yana harbin kan mai tsautsayi daga bisani ya tada wanda ke jikinsa.

Kawo yanzu babu wanda ya san dalilinsa na aikata hakan, amma wasu rahotanni na cewa daman matashin ya tsani kwalejin kuma yana son daukar fansa.

Rahotonnin farko sun nuna cewa fashewar ta faru ne ta dalilin fashewar iskar gas.

Amma wani jami'in tsaron Rasha ya ce wannan lamari aikin 'yan ta'adda ne.

Sergei Melikov ya shaida wa kafar yada labarai ta Rasha mai suna Tass cewa bam din ya tashi ne sanadiyyar abin fashewa.

Wani jami'in tsaro ya ce yawancin wadanda abin fashewar ya shafa dalibai ne na kwalejin fasahar, wadda makaranta ce ta koya wa matasa sana'a.

Masu bincike sun wallafa wani bayani inda suke cewa abin fashewar mai dauke da karikicen karafa ya tashi ne a wani wajen cin abinci.

Daraktan kwalejin wacca ba ta wurin lokacin da abin ya faru, ta fada wa 'yan jaridar kasar Rasha cewa wasu baki sun shigo cikin kwalejin.

Har ila yau ta kwatanta masalar da kawanyar da ta faru a shekarar 2004 a wata makaranta a yankin Beslan, inda mutane 330 suka rasa rayukansu.

Ta ce "akwai gawarwaki da yawa na dalibai da na kananan yara, wannan hari ne na ta'addanci," in ji ta.