Buhari ya kira taron shugabannin yankin Tafkin Chadi kan Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu ya kira wani taro don ganawa da shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi ranar Alhamsi 29 ga watan Nuwamba a N'Djamena babban birnin Chadi kan batun Boko Haram
A wata sanarwa da shugaban ya fitar a shafinsa na Twitter yayin da yake ziyara a jihar Borno ranar Laraba, shugaban ya ce: "A matsayina na shugaban babban taron koli na shugabannin Kasashen Yankin Tafkin Chadi LCBC, ina kira ga taron ganawa da shugabannin kasashen yankin na kwana guda.
"Domin a sake duba batun yanayin tsaro a yankunan da rikicin Boko Haram ke shafa, da kuma inganta Rundunar Hadin Gwiwa ta kasa da kasa don ceto yankin daga halin da yake ciki."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Shugaban ya ce ya gayyaci shugabannin kasashen Chadi da Kamru da Nijar da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da kuma Jamhuriyar Benin don su halarci taron.

Tsaro a yankin Chadi
Yankin Tafkin Cahdi wanda ya hada kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi ya sha fama da rikice-rikice da tabarbarewar al'amura sakamokon hare-haren kungiyar Boko Haram.
Rikicin Boko haram ya hana noma ko samun damar kai dabobb mashaya.

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma rikicin ya hana masu kamun kifi damar zuwa tafkin da kasashen Kamaru da Nijar da Najeriya da kuma Chadi ke amfani da shi.
Rikice-rikicen kungiyar boko Haram sun yi mummunar illa ga yankin, wanda dama yake daya daga cikin wadanda ke fuskantar talauci a duniya.
Kusan shekara goma aka shafe ana fama da rikicin na Boko Haram.

Waiwaye kan rundunar hadin gwiwa ta Tafkin Chadi

A watan Yunin 2015 ne shugabannin kasahsen yankin tafkin Chadi suka gana a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, inda suka sha alwashin bayar da $30m domin samarwa dakarun makamai da sauran kayan aiki na yaki da kungiyar ta Boko Haram.
Shugabannin sun amince a kafa hedikwatar dakarun hadin-gwiwar a birnin N'Djamena na kasar Chadi.
Sai dai a lokacin Shugaba Buhari ya ce kasarsa ce ya kamata ta rike shugabancin rundunar ta hadin-gwiwa da za a kafa domin yaki da kungiyar Boko Haram
Muhammadu Buhari ya ki amincewa kasashen su rika karba-karba a shugabancin rundunar, yana mai cewa hakan zai bai wa Boko Haram damar ci gaba da kai hare-hare.
Sai dai wasu masu sharihi na ganin rundunar ba ta taka rawar da ta kamata a yakin da ake yi da Boko Haram, saboda wasu matsaloli da shuka hada da rashin isassun kudade da kuma kayan aiki.












