Me ya sa yara ke yawan fadawa masai a Afirka Ta Kudu?

Aboka Micheal da iyalinsa sun halarci jana'izar Micheal Komape

Asalin hoton, Gallo

Bayanan hoto, Abokan Micheal da iyalinsa sun halarci jana'izar Micheal Komape

A makonsa na farko a makaranta, Michael Komape mai shekara biyar ya fada cikin masai a arewacin kasar Afirka ta kudu.

Al'amarin ya faru ne a watan Janairu na shekarar 2014 kuma ya kasance ranar da mahaifinsa James Komape ba zai taba mantawa da ita ba.

Ya kai wakiliyar BBC makarantar da ke kauyen Chebeng kuma har yanzu yana cikin wani mawuyacin hali.

"A lokacin da na je bakin shaddar, na hango karamin hannunsa," in ji shi.

"Wasu mutane sun tsaya suna kallon shaddar, babu wanda ya yi tunanin ciro shi. Na ji takaici sosai game da abin da na gani.

"Ba dai dai ba ne a samu wani da ya rasa ransa ta wannan hanyar."

Ya yi shuru na wasu dakikoki kafin ya ci gaba.

"Ya rika kokarin ganin cewa an kai masa dauki ko kuma ya kubatar kansa. Har yanzu ina jin wani iri idan na tuna cewa dana ya mutu shi kadai kuma watakila ya rika jin tsoro."

Iyayen Michael, James Komape da Rosina Komape
Bayanan hoto, Iyayen Michael Komape za su daukaka kara kan hukuncin da wata kotu ta yanke, wadda ta yi watsi da bukatarsu ta diyya

Mr Komape ya sunkuyar da kansa.

Ya zira ido kan wani jan bulo da aka saka a kan masai.

Bakin masan ya rufta ne lokacin da Micheal ya zauna akai a cewar hukumomi.

Sai dai wannan matsala ce da ake fuskanta a wasu makarantu da ke kasar.

Duk da cewa kowa na da hakkin a samar musu da muhali mai tsafta kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, amma dalibai ba su da wani zabi illa su yi amfani da masai.

Presentational grey line

Makaratun masu masai a kasar Afirka ta kudu

Taswirar kasar Afrika ta kudu
Bayanan hoto, Taswirar kasar Afrika ta kudu wadda ta nuna lardunan Limpopo da KwaZulu Natal da Eastern Cape
  • Makaratu fiye da 4,500 ne suke da masai a cikin makarantu 25,000 da ke kasar baki daya
  • Akasarinsu an kafa su ne da wani karfe mai arha sosai kuma babu inganci a kan yadda aka gina su, kuma a bude ake barinsu
  • Matsalar ta fi kamari a lardunan Eastern Cape da KwaZulu-Natal da Limpopo in ji ministar ilimi Angie Motshekga
  • Makaratu 61 ake da su a lardin Eastern Cape kuma babu ba haya a cikinsu kuma makarantu 1,585 kadai ne suke da masai
  • Makwabciyar KwaZulu-Natal na da masai 1,379 da ake amfani da su
  • Lardin Limpopo, inda a nan ne Michael Komape ya rika zuwa makaranta na da wurin baya haya 932 marasa inganci.
Presentational grey line

Shin ya aka yi lamura suka tababbare?

Wasu masu sharhi sun dora alhakin hakan kan wariyar launin fata, saboda a karkashin mulkin farar fata marasa rinjaye babu wani kason da aka ware domin inganta makarantun da aka kafa domin marasa galihu, wadanda galibi yaran bakar fata ne.

Sun kuma dora alhaki kan gazawar gwamnati wajen kula da makarantun yadda ya kamata.

A cikin wannan shaddar ne ta makarantar Mahlodumela Michal Komape ya rasu

Asalin hoton, Gallo

Bayanan hoto, A cikin wannan shaddar ne ta makarantar Mahlodumela Michal Komape ya rasu

A gidansu da ke wajen garin Polokwane, a lardin Limpopo, iyalin Komapes sun shaida wa BBC cewa suna son a yi mu su adalci dangane da mutuwar Michael.

Tare da taimakon wani kamfanin lauyoyi masu kare hakkin bil'dama mai suna Section 27, iyayen Micheal na shirin daukaka kara a kan hukuncin da wata kotu ta yanke, wadda ta yi watsi da bukatarsu ta neman diyya kan abun da ya faru.

Suna tuhumar ma'aikatar ilimi ta lardin Limpopo da sakaci.

Hoton Michael Komape

Asalin hoton, Kirsten Whitefield

Bayanan hoto, Kamfanin Section27 na taimakawa iyalin Komapes daukaka kara gaban kotu

"Abin da ya faru da iyalin Komape abin takaici ne kuma ya fito fili ya nuna karara halin da makarantun suke ciki a kasar," kamar yadda Zukiswa Pikoli jami'a a kamfanin Section27' ta shaida wa BBC.

"Mun kadu lokacin da muka ji labarin abin da ya faru da Micheal. Babu yadda zamu yi mu ce ba za mu taimaka musu ba."

Ms Pikoli ta ce kamfaninsu na da niyyar daukaka kara a kotun kundin tsarin mulkin kasar wadda ita ce kotun koli a Afirka Ta Kudu.

Daliban makarantar frimare ta Sebushi
Bayanan hoto, Wasu dalibai na kusa da wurin da Micheal Komape ya mutu kuma a yanzu suna yi wa junansu rakiya

Sai dai iyalin Komapes ba su kadai ba ne suka rasa yaronsu a cikin wannan yanayi.

A farkon shekarar da mu ke ciki wata yarinya 'yar shekara biyar ta fada a cikin masai a lardin Eastern Cape.

Lumka Mkhethwa ta bata a makarantar frimare ta Luna a watan Maris da ya gabata.

An sanar da kauyen kuma an shafe daren ranar ana nemanta amma ba a ganta ba.

Bayan kwana daya da faruwar lamarin ne 'yan sanda suka koma makarantar, inda nan aka yi mata gani na karshe.

Wasu karnuka ne suka yi musu jagora inda ka gano gawarta a cikin masai.

Bayan muturwarta ne sabon shugaban kasar Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya nemi a kawar da amfani da masai kafin shekarar da mu ke ciki ta kare.

Sai dai shiri ne da zai bukaci makudan kudi.

'Shekaru da ka shafe babu kula'

Rahoton gwamnatin hadin gwiwa ya yi hasashen cewa za a bukaci kudi fiye da rand biliyan 11 kwatankwacin dala miliyan 876, kuma kudin da take son ta tara tare da taimakon kamfanoni masu zaman kansu.

"Mun dauki mataki ne kan shekarun da ake yi ba a kula da makaruntu ba sai dai za a samu sauyi, ko da yake a hankali ne za a kawo sauyin," in ji Elijah Mhlanga, jami'i a ma'aikatar ilimi.

Michael Komape

Asalin hoton, Supplied by Komape family

Bayanan hoto, Mutuwar Michael Komape ta sa mutanen yankinsa sun farga

"Lamuran nan biyu da suka faru abin takaici ne, amma muna fatan wannan ya nuna wa kowa yadda girman matsalar ta ke," in ji shi.

"Akwai wasu da suka nuna aniyyar taimaka mana da tallafi.

"Aniyyarmu ita ce mu ga an kiyaye tsaron lafiyar yara a makaruntunmu."

Malamai masu sintiri

A wani kauye da ke lardin Limpopo, labarin rasuwar Micheal ta sauya yadda ake tafiyar da al'amura a cikin makarantu.

An tsafttace muhalli a makarantar firame ta Sebushi.

A bayan wani wuri mai ciyawa da aka yanka ne aka gina masai masu inganci.

Akwai wurin da aka ware domin malamai su rika sa ido kan daliban da za su yi amfani da su.

"Karfe shida na ko wacce safiya akwai malamin da ke sintiri domin ya ga wanda ya shiga da kuma wanda ya fito," in ji Joseph Mashishi, ahugaban makarantar.

Salgar da aka gina bayan muutuwar Michael
Bayanan hoto, Salgar da aka gina bayan mutuwar Michael

"Ba ma son abin da ya faru da iyalin Komape ya auku a makarantarmu. Ba daidai ba ne yaro ya rasa ransa a cikin masai, babu tausayi a ciki."

Mutane da dama a kauyen Michael sun farga.

Sun fara fafutukar ganin cewa an samar mu su da sabbin ba-haya a dukkanin makarantun da ke yankin domin tunawa da marigayin.