Shin wane martani Nigeria ta mayar kan kalaman Trump?

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta game da kalaman Trump.

Gwamnatin Najeriya ta bi sahun wasu kasashe da kungiyoyi da ke mayar da martani a kan kalaman da aka ambato shugaban Amurka, Donald Trump ya fada a kan kasashen Afrika.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta game da kalaman na Mista Trump.

Ministan harkokin wajen Najeriya Geofrey Onyeama ya bayyana kalaman da cewa na tozarta wa ne ga kasar kuma abu ne da ba za ta lamunta ba.

Ministan ya bayyana hakan ne a jiya Litinin bayan ya aika sammaci ga jakadan Amurka da ke Abuja domin ya yi masa bayani a kan kalaman na shugaba Trump.

A makon jiya ne rahotanni suka ambato Mista Trump na bayyana kasashen Afrika a matsayin "wulakantattu kasashe".

Batun dai na ci gaba da janyo cece-kuce, duk da cewa shugaban na Amurka ya musanta furta kalaman.

Sai dai jakadan Amurka bai samu halartar ganawar da aka yi a jiya a birnin Abuja ba, amma ya samu wakilcin mataimakinsa David Young.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Dakta Tope Ade Elias-Fatile ya shaidawa BBC cewa ministan harkokin wajen Najeriya ya nemi karin haske game da gaskiyar kalaman na Trump.

"Ministan ya jaddada cewa idan da gaske ne shugaba Trump ya fadi hakan, to kalamai ne na tozartawa da matukar ban takaici kuma abu ne da Najeriya ba zata amince da shi ba".

"Musamman idan aka yi la'akari da irin kyakkyawar dangantakar da ake da ita yanzu a tsakanin Najeriya da Amurkar," a cewar Mista Elias-Fatile.

An yi zanga-zangar kyamar Trump a Haiti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi zanga-zangar kyamar Trump a Haiti

Sai dai kuma a martanin da ya mayar ga ministan harkokin wajen, Mista Elias-Fatile ya kara da cewa jakada Young ya yi nuni da cewa akwai bayanai masu sabawa juna daga wadanda suka halarci ganawar wanda ya shafi gaskiya ko akasin hakan kan kalaman na shugaba Trump.

Jakadan ya kuma kara da cewa gwamnatin Amurka za ta ci gaba da daukar 'yan Najeriya da matukar muhimmanci, haka kuma tana mutunta kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsu, inda ta ke fatan dangantakar ta fi hakan a nan gaba.

Tun a ranar juma'ar da ta gabata ne dai kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana kaduwarta da matukar bacin ranta a kan kalaman da aka ambato shugaban na Amurka ya fada. Inda ta nemi shugaban ya nemi gabafar kasashen na Afirka ya kira a matsayin masai.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai aka ruwaito Mista Trump ya furta kalaman a wajen wani taron da ya yi da 'yan majalisa a kan wata doka da ta shafi 'yan gudun hijira. Sai dai shugaban na Amurka ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi amfani da kalaman.

Kafafen yada labarai da dama na Amurka ne suka fara wallafa kalaman na Mista Trump suna masu ambato wasu daga cikin wadanda suka halarci ganawar da shugaban ya yi da 'yan majalisar.

Ko da yake fadar White House ba ta musanta wadannan rahotanni ba.

Trump ya taba ganawa da shugabannin Afirka a taron G7 a Italiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Trump ya taba ganawa da shugabannin Afirka a taron G7 a Italiya

Kasar Bostwana ita ma ta aika sammaci ga jakadan Amurka da ke kasar, inda ta nemi ya yi bayani game da kalaman na shugaban Amurka.

Kakakin hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana kalaman da cewa na nuna banbancin launin fata ne.