'Sai iyaye da al'umma sun hada kai za a yaki shaye-shaye'

Asalin hoton, Getty Images
Wasu masu ruwa da tsaki a harkar yaki da shaye-shaye a Najeriya sun ce babu wani matakin da zai magance matsalar, har sai iyaye da al'umma baki daya sun hada kai wajen yakarta.
Sun bayyana ra'ayin nasu ne a wajen wani taro da majalisar dattawan kasar ta shirya a birnin Kano don samar da mafita.
Baba Umar Galadima, shi ne mataimakin shugaban kungiyar fadakar da matasa a kan illolin shaye-shaye da aka fi sani da Youth Awareness Forum on Drug Abuse, a Kano.
Ya kuma shaida wa Ibrahim Isa na BBC cewa shi ma ya yarda da wannan ra'ayin.
Sai ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron yadda hirar tasu ta kasance:








