Dararen da za ku iya kallon gilmawar ɗaruruwan taurari masu wutsiya a 2025

A ranakun ganinsa na ƙololuwa, kuma lokacin ganinsa da ya dace, za a iya ganin taurari masu wutsiya masu haske kusan 120 duk sa'a ɗaya.

Asalin hoton, Cheng Luo/NASA

Bayanan hoto, A ranakun ganinsa na ƙololuwa, kuma lokacin ganinsa da ya dace, za a iya ganin taurari masu wutsiya masu haske kusan 120 duk sa'a ɗaya, kuma za su shigo duniya da saurin kilomita 40 duk daƙiƙa, a cewar NASA.
Lokacin karatu: Minti 4

Idan ka kasance mutum mai son kallon abubuwan ban sha'awa a sararin samaniya, to lallai za ka so karanta wannan labari.

Lokaci na farko na ganin taurari masu wutsiya na shekarar 2025, wanda ake kira Quadrantids, zai kai kololuwa a ranar 3 da huɗu na watan Janairu kuma za a iya ganinsa da ido. Ya fara ne tun ranar 28 ga watan Disamba, kuma zai cigaba har 12 ga watan Janairu.

A cewar hukumar sanya ido kan duwatsun da ke yawo a sararin samaniya na duniya (IMO), ana sa ran ruwan taurarin zai zama ''wanda zai fi kowanne a wannan shekarar''.

A ranakun da za a fi ganinsu, kuma a daidai lokacin da za su kwararo zuwa sararin samaniyar duniyarmu, za a iya tsinkayar taurari masu wutsiya kusan 120 a kowace sa'a ɗaya, kuma za su shigo sararin duniya ne suna gudun kilomita 40 cikin duk daƙiƙa ɗaya, a cewar hukumar sararin samaniya ta Amurka, NASA.

Sai dai ba lallai koda yaushe a samu yawan hakan ba saboda gajeren lokacin ganinsa na sa'a 6 da kuma yanayi maras kyau da ake fuskanta a farkon watan Janairu, in ji IMO.

Lokacin gilmawar taurari masu wutsiya da yawa, wanda ake kira ‘Quadrantids’ turance, ya samu sunansa ne daga Quadrans Muralis, wata ƙungiyar taurari da aka gani a karshen ƙarni na 18.

An yi imanin cewa wani masanin taurari ɗan Italiya, Antonio Brucalassi ne ya fara ganin su a shekarar 1825, wanda ya hango taurari masu wutsiya suna haskakawa daga wannan ɓangaren na sararin samaniya.

Quadrantid na ɗaya daga cikin ruwan taurari masu wutsiya da ake samu daga ɓurɓushi na asteriod (wanda duste ne) yayin da wasu kuma ana samun su daga Comets (wanda ƙanƙara ne da kuma kura).

Yadda ake ganin ruwan taurari masu wutsiya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An fi iya ganin irin wannan yanayi ne a ɓarin duniya na arewa, ɓangaren sararin samaniya da ake tunanin taurari masu wutsiyan na fitowa daga wurin, idan ya kasance ya yi sama sosai da layin da ake ganin duniya da sararin samaniya sun haɗu.

Abin takaici, in ji hukumar IMO shi ne, '' kaɗan daga cikin wannan abu ne kawai ake iya gani daga ɓarin duniya na kudu'', saboda ko dai hasken ya yi kaɗan ko kuma ba a ma iya gani saboda gajerun darare da ake samu a lokacin zafi.

Wasu daga cikin taurarin masu wutsiya da suke birgewa, ana iya ganin su daga tsakiyar gari, sai dai wanda zai fi ƙayatarwa shi ne wanda ke nesa da hasken da ke fitowa daga birane.

''Iya duhun da sararin samaniyan ke da shi, shi zai ƙara maka damar ganin taurarin da ba su da haske sosai,'' a cewar dakta Ashley King, wani masanin kimiyyar duniyoyi kuma ƙwararre a ilimin duwatsun da ke sararin samaniya, wanda ke a gidan ajiyar kayan gargajiya na tarihi da ke Landan.

Cikkaken wata na iya haska sararin samaniya, lamarin da zai sa ganin taurarin masu wutsiya ya ƙara yin wahala, a don haka damar ka mafi kyau ita ce idan lokacin da aka fi ganin su ya zama a farkon kamawar wata.

A ranakun da aka fi ganin su, watan zai sauka tun da farkon yammaci, wanda zai rage yiwuwar samun haske mai yawa da zai kawo tsaiko ga kallon taurarin masu wutsiya.

Ba a buƙatar amfani da wata na'ura ta musamman wajen kallon su, sai dai yin haƙuri ma na da muhimmanci.

A don haka, ka nemi wuri mai duhu da ke nesa da hasken cikin gari, ka kwanta a ƙasa ta yadda kafarka za ta kalli arewa maso yamma, kuma ka ba idanunka mintuna 15 zuwa 20 su saba da duhun.

''Ba lallai ka ga wani abu a mintuna goman farko ba,'' in ji dakta King.

''Amma a lokacin da idonka ya saba da duhun, za ka fara ganin su kaɗan-kaɗan. saboda haka, kar ka karaya tun da wuri.''

Me ke janyo kwararowar taurari masu wutsiya?

Taurari masu wutsiya na Quadrantid.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a iya ganin kwararar taurari masu wutsiya na Quadrantid har ranar 12 ga watan Janairu

Duk da ana kiran su ''taurari masu wutsiya'', ba taurari ba ne kwata-kwata. Wasu ƙananan ragowar abubuwa ne daga duniyoyi da ke ƙonewa idan suka biyo ta duniyarmu.

''A yayin da suka fito daga sararin samaniya zuwa duniya, waɗannan dunkulallun ƙurar suna haɗuwa da wasu ƙwayoyin a iskar duniya. Suna ɗaukar zafi idan suka haɗu, wanda ke samar da wani haske mai ƙayatarwa da muke gani,'' a cewar dakta King.

Ana samun ruwan taurari masu wutsiya ne a lokacin da duniya ta bi ta cikin ƙananan duwatsun sararin samaniya da ake kira meteoroids.

Lokacin kolokuwar ganin ruwan taurarin masu wutsiyar na faruwa ne a lokacin da duniya ta shiga ɓangaren da ke cunkushe da ɓurɓushin duwatsun wanda ke sa a gan su da yawa.

Kada ku damu idan ba ku samu ganin Quadrantids ba, za a samu wasu ruwan taurari masu wutsiyan a cikin shekarar nan - duk da dai babu wanda zai kai wannan yawa - waɗanda kuma za a fi ganin su ne a ɓarin duniya na kudu.