'Me ya sa ake ce-ce-ku-ce kan yarjejeniyar Samoa a Najeriya?

Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu
Tun bayan ɓullar labarin sanya hannu da Najeriya ta yi kan yarjejeniyar Samoa, 'yan ƙasar keta ce-ce-ku-ce game da yarjejeniyar musamman kan wasu batutuwan da ta ƙunsa.
Ƙasashen da ke cikin yarjejeniyar su ake kira 'Organisation of African, Caribbean and Pacific States' (OACPS).
A ranar 15 ga watan Nuwamban 2023, ana cimma yarjejeniyar tsakanin ƙasashen ƙungiyar Tarayyar Turai da na Afirka da ƙasashen yankin Caribbean da kuma na yankin Pacific da aka sanya wa suna 'yarjejeniyar Samoa'.
Yarjejeniyar ta ƙunshi ƙasashen Tarayyar Turai 27 da kuma ƙasashe 79 daga nahiyar Afirka da yankin Pacific da na Caribbean.
Jimillar mutanen ƙasashen da ke cikin yarjejeniyar sun haura mutum biliyan 1.2.
Me yarjejeniyar Samoa ta ƙunsa?
Ƙungiyar OACPS ta yi tanadin cewa yarjejeniyar Samoa ta ƙunshi abubuwa da dama da suka dangancin dimokaɗiyya da shugabanci da daidato tsakanin jinsi da kuma bin doka.
Manufar yarjejeniyar ita ce taimaka wa ƙasashen da ke cikinta gina kansu don inganta tattalin arzikinsu.
Majalisar Tarayyar Turai ta ce an gina yajejeniyar Samoa kan manyan batutuwa shida
- 'Yancin ɗan'adam da Dimokraɗiyya da gwamnati da
- Zaman lafiya da tsaro
- Ci gaban al'umma da tafiya tare
- Ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa
- Inganta muhalli da sauyin yanayi
- Batun cirani da zirga-zirga.
An cimma yarjejeniyar ce a taron ministocin ƙungiyar ƙasashen da aka gudanar kafin bikin sanya hannu kan yarjejeniyar da aka gudanar a Samoa.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen bunƙasa harkokin zuba jari, da hulɗar kasuwanci tare da samar da ci gaba da zaman lafiya a ƙasashen da ke cikin yarjejeniyar.
Babban sakataren ƙungiyar 'OACPS - EU, Georges Rebelo Pinto Chikoti, ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen samar ci gaba tsakanin ƙasashen.
Me ya sa Najeriya ta sanya hannu kan Yarjejeniyar?
A ranar 28 ga watan Yunin 2024 ne Najeriya ta bi sahun ƙasashen ƙungiyar wajen sanya hannu kan yarjejeniyar.
Ƙungiyar OACPS ce ta tabbatar da hakan cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X.
“A yau Najeriya ta bi sahun ƙasashe 72 wajen saka hannu kan yarjejeniyar Samoa. Amb. Obinna Chiedu Onowu ne ya wakilci ƙasar wajen sanya hannu kan yarjejeniyar a sakatariyar ƙungiyar OACPS da ke birnin Brussels.”, kamar yadda saƙon ya nuna.
Ministan watsa labaran ƙasar, Muhammmad Idris ya shaida wa BBC Hausa cewa yarjejeniyar ta ƙunshi ayyukan ci gaban al'umma ne, kuma an yi ta ne a tsakanin ƙasashen Afrika da na yankin Caribbean, da mutanen Pacific wato OACPS.
Yarjejeniyar ta ƙunshi auren jinsi?
Wannan shi ne batun da ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar, bayan da aka yi zargin cewa bai wa masu auren jinsi kariya na daga cikin sharuɗan yarjejeniyar.
Akwai zargin cewa yarjejeniyar ta ce dole ne gwamnatin Najeriya ta bayar da dama ga masu auren jinsi idan har tana son amfana da tallafin dala biliyan 150 daga cikin ƙunshin yarjejeniyar.
Wannan batu dai ya janyo zazzafar muhawar tsakanin 'yan ƙasar, inda mutane da dama suka yi ta sukar yarjejeniyar.
Kasancewar kundin tsarin mulkin ƙasar ya haramta auren jinsin.
Me gwamnatin Najeriya ta ce?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwamnatin Najeriyar ta musanta wannan zargi, tana mai cewa sai da ta tabbatar da cewa yarjejeniyar ba ta saɓa wa dokokin ƙasar ba, kafin ta yarda ta saka hannu a kai.
Minisitan watsa labaran ƙasar, Muhammmad Idris ya shaida wa BBC Hausa cewa yarjejeniyar ta ƙunshi ayyukan ci gaban al'umma ne.
Ya ci gaba da cewa "Akwai ƙa'idoji har 103 da aka cimma kan wannan yarjejeniya, amma babban al'amari da ya kamata a fahimta a nan shi ne, an yi waɗannan yarjejeniyar ne bisa tsarin shari'a da zai ba da damar haɗin gwiwa tsakanin OACPS da Tarayyar Turai domin cigaban al'umma, da daƙile sauyin yanayi, da samar da kuɗaɗen zuba jari, ba wai yadda mutane ke ta yaɗawa ba.
Ministan yaɗa labaran ya ce 'Ko kaɗan babu gaskiya a cikin wannan zargi, don kafin mu saka hannun kan waɗannan ƙa'idoji 103 sai da aka kafa kwamiti da ya yai tatsa da tsifa a kansu, wanda ministan kasafin kuɗi Atiku Bagudu ya jagoranta.
''Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da ministan harkokin wajen Najeriya, da Ministan shari'a wanda kuma sai da suka tabbatar da cewar babu wata ƙa'ida daga cikin ƙa'idojin da ta ci karo da dokokin Najeiya sannan aka amice da saka hannun" in ji ministan.
Ya ƙara da cewa "ya zama wajibi mu tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa gwamnatin Bola Tinubu ba za ta saka hannu kan wata yarjejeniya ba da za ta ci karo da muradan mutanenten ƙasar nan ba ".
Muhammad Idris ya ce tun da fari Najeirya ta ƙi amincewa ta sa hannu kan yarjejeniyar ne don kauce wa kisto da ƙwarƙwata da zai kai ga faɗa wa tarkon irin zargin amincewa da abin da ya saɓa da dokokin ƙasar.
"In ka ga an ƙi amincewa da abu, to akwai dalili, misali an duba an ga akwai wasu abubuwa da suka saɓa da dokokinmu, wadannan dole ne a tsaya a tantance su a zare su, a fitar da su daga cikin yarjejeniyar" Inji minsitan.
Ya kuma ce 'Yanzu an kawo lokacin da yarjejeniyar ba ta ci karo da addini, ko zamantakewarmu, ko al'adunmu, ko dokokin ƙasarmu ba, don haka ina mai tabbatar wa da al'ummar Najeriya cewa, su kwantar da hankulansu, gwamantin Bola Tinubu ba za ta taɓa amincewa da abin da ya ke cin karo da dokokin ƙasar nan ba".
A shekarar 2014 Najeriya ta amince da dokar haramta alaƙar aure tsakanin jinsi ɗaya, abin da ke nufin luwaɗi da maɗigo haramtattu ne a ƙasar.











