Abin da dokar da ke son ɗaure ƴan Daudu a Najeriya ta ƙunsa

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Daudu musamman maza masu shiga irin ta mata da mata da ke shiga irin ta maza za su fuskanci hukunci a Najeriya.
Wannan na cikin wani ƙuduri da aka gabatar a gaban Majalisar Wakilan Najeriya da ke son a yi wa Dokar Haramta Auren Jinsi kwaskwarima inda wani ɗan majalisa ya nemi a haramta daudu a ƙasar.
A ranar Talata ne 'yan majalisar suka yi wa ƙudirin karatun farko. Sai sun yi karatu na biyu da na uku sannan ya zama doka.
Ɗan majalisa mai wakiltar Toro daga Jihar Bauchi, Umar Muda Lawal ne ya gabatar da kuɗirin a majalisar inda ya nemi a haramta daudu a fili ko kuma a ɓoye.
Tun 2014 tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sanya hannu kan dokar haramta auren jinsi ɗaya.
Ƴan majalisa wakilai sun amince da dokar a 2013.
Babbar manufar dokar shi ne haramta auren jinsi ɗaya a Najeriya.
Dokar kuma ta haramta masu jinsi ɗaya kasancewa tare a matsayin masoya da haramta duk wani biki na nuna soyayyar jinsi ɗaya.
Dokar na ɗauke da ɗaurin shekara 10 ga duk wanda aka kama ko ƙungiya da ke goyon bayan ayyukan auren jinsi ɗaya.
Dokar a taƙaice ta haramta maɗigo da luwaɗi da duk wani mataki na neman sauya jinsi.
Me kwaskwarimar dokar ta ƙunsa?
A sashe na bakwai na dokar, ɗan majalisar ya nemi a hukunta ƴan daudu musamman mazan da ke shiga da kuma kwaikwayon mata ko kuma matan da ke kwaikwayon maza.
Dokar ta ce, "mutum ya aikata laifi idan har fito bainar jama'a ko a asirce yana ɗabi'u irin na ƴan daudu.
Amma wannan bai shafi waɗanda ke wasan kwaikwaiyo ba.
Hukuncin da dokar ta ƙunsa
Dokar ta nemi a saka ɗaurin wata shida a cikin dokar ko kuma tarar naira 500,000 ga duk wanda aka kama a matsayin ɗan daudu.
Ɗan majalisar na so a ƙara wani ƙaramin sashe na 4 cikin baka a cikin Dokar Haramta Auren Jinsi ta 2013 da zai ayyana cewa: "Duk wanda aka kama yana aikata daudu ya yi laifin da zai iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na wata shida ko kuma tarar N500,000."
Sannan za a kama duk wanda aka kama yana daudu a bayyane ko a ɓoye.
Me Mutane ke cewa?
Tuni wasu ƴan Najeriya masu adawa da dokar suka fara tsokaci.
Daga cikin martani akwai na ɗaya daga cikin mai rajin kare ƴan maɗigo da luwaɗi da ya sauya halitta zuwa mace kuma ta yi fice a kafofin sada zumunta Okuneye Idris Olarenwaju, da ake kira Bobrisky.
Bobrisky ta rubuta a shafinta na Twitter tana ƙalubalantar kudirin dokar da kuma majalisar wakilan Najeriya.
Ta yi shaguɓe inda ta lissafa abubuwa biyar tana cewa amfanin dokar za ta magance ƙalubalen tsaro da wutar lantarki da kawo ƙarshen yajin aikin ASUU da yadda ake ɗaukar Najeriya a ƙasashen waje da kuma raguwar farashin kayayyaki.

Asalin hoton, Twitter
Wani mai amfani da Twitter Sylvester Adejo ya ce: "duk da ba na goyon bayan ɗabi'ar, amma ina ganin akwai abubuwan gaggawa da suka fi wannan.
"A wannan ƙasar, yara na gida, matsalar tattalin arziki na cikin wani hali da sauransu, abin da ya kamata mu fara diba wa kenan mu kyale wadannan mutanen a yanzu."

Asalin hoton, Fcebook
Ekene ya ce: "ƴan Daudu ba laifi ba ne, domin shi ne mafi kankantar matsalar Najeriya. Mayar da hankali kan ƴan Daudu bai dace ba maimakon su mayar da hankali kan yaƙar ƴan bindiga. "

Asalin hoton, Twitter











