Gwauron da ya wallafa hotonsa a allon talla don neman matar aure

Asalin hoton, Muhammad Malik
Wani gwauro na amfani da katafaren allon talla don neman matar aure.
Muhammad Malik mai shekara 29 na ƙoƙarin sanar da gwauraye 'yan uwansa a Landan da Birmingham na Birtaniya cewa yana neman matar aure.
Tallan na cewa: "Ku kuɓutar da ni daga auren dole."
Ya ce ba wai yana adawa ne da tsarin auren ba amma yana so ya "jarraba neman wata da kansa".
Sai dai zuwa yanzu haƙansa bai cimma ruwa ba, yayin da mazaunin Landan ɗin kuma ƙwararre a harkokin banki yake fatan sabon shafin intanet na findmalikawife.com zai taimaka masa.
Mista Malik ya ce ya samu ɗaruruwan saƙonnin soyayya tun bayan saka allunan tallan a ranar Asabar.
"Ban samu cikakken lokacin duba su ba har yanzu," a cewarsa. "Akwai buƙatar na ware lokaci - ban gama tunani kan haka ba tukunna."

Asalin hoton, Muhammad Malik
Malik ya ce ya yi yunƙurin zuwa zance wajen mata daban-daban ta hanyoyi daban-daban kafin saka allunan tallan amma hakan ba ta yiwu ba.
"Ni ɗan ƙabilar Desi Pakistan ne," in ji shi, "saboda haka abu na farko da ake faɗa mana shi ne ƙarfin ikon gwaggwanni ('yan uwan uwa ko uba). Sai dai wannan tsarin "ba me ɓullewa ba ne".
Sai kuma aka samu manhajojin soyayya da kuma tarukan haɗuwa da 'yan mata, amma ya ce sun sa yana "jin kunya sosai".
A ƙarshe dai, wani abokinsa ya ba shi shawarar ya gabatar da kansa. Mista Malik ya ce: "Na yi tunanin mene ne a ciki - 'wace matsala ce za ta faru'?"
Ana sa ran allunan tallan za su ci gaba da zama har zuwa 14 ga Janairu. Sannan kuma yana samun goyon bayan danginsa, inda iyayensa suka amince tun daga farko.
Sai dai ya ce "sai da na ɗan lallaɓa mahaifiyata".
Mista Malik duk wadda za ta aure shi sai ta kasance Musulma sannan kuma ta iya zama da 'yan uwansa.











