Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa masu gajeren barci suka fi masu dogon barci karsashi
Barcin sa’o’i nawa ya kamata mutum ya yi kafin ya samu koshin lafiya?
Idan amsar ka ita ce sa’o’i takwas, to ba lallai ya zamanto daidai ba idan aka yi la’akari da sabbin bincike na kimiyya.
"Wannan ai rashin fahimta ne. Kamar a ce kowa tsayinsa ya kai mita 1.65.
Idan kuma mutum gajere ne, za a samu matsala," a cewar malami a Sashen Nazarin Cutukan Kwakwalwa da kuma Cutar Laka da ke Jami’ar Jihar California a Amurka.
Ba dukkanmu ne ke bukatar yawan barci ba domin samun koshin lafiya. Kuma ba batun dabi’a ba ce ko zabi.
Abin yana da dangantaka da kwayar halittar mutum.
Za a iya cewa wasu sun guji yin gajeren barci. Wannan na nufin cewa idan baccin awa uku zuwa shida kadai za su yi, su kuma farka su ji garau komai lafiya.
"Akwai wasu mutane da ake kira masu ‘mugun barcin’, kuma ina ga hakan yana da kyau.
Suna gudanar da rayuwarsu lami lafiya tare da yin gajeren barci , inda zaka ga suna aiwatar da ayyukansu na yau da kullum cikin zimma.
Kuma gaskiya ne hakan yana fa’ida ba mai kadan ba a wannan duniyar ta mu ta aiki da muke ciki,’’ a cewar Dr Ptacek.
Masu mugun barci
A tsawon shekara 25 da suka gabata, Dr Ptacek da jami’ansa sun yi bincike kan irin yanayin barci na iyalai sama da 100.
"A lokacin da muka fara, mun mayar da hankali kacokan a kan me ya kamata ya zama ma’auni kan abin da muke kira da 'mutumin da ya ci gaba da barci'. Irin wadannan mutane kuma ana kiransu da ‘masu tashi kan kari’.
Sukan kwanta da wuri su kuma tashi da wuri.
Wasu mutane na shiga idonmu saboda tashi da wuri, amma ba za su kwanta barci a kan lokaci ba don cika ka’idojinmu.
A lokacin ne muka samu labarin cewa akwai wasu iyalai da suke da ‘yan safiya da kuma ‘yan dare.
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Hakan ne ya sa muke tunanin cewa watakila akwai wasu abubuwa na iyalan – kamar na yin gajeren barci – wanda ke sa wasu ba sa kwanciya da wuri, amma za su tashi da wuri, su kuma gudanar da aiki ba tare da wata matsala ba.
Wasu dai sun bayyana abubuwa hudu na kwayoyin halittar mutum da suka danganci yin barci kadan, sai dai yakan iya zarta wannan.
Matsalar ita ce kwayoyin halittar sun bambanta.
Dr Ptacek ya kiyasta cewa watakila mutum daya cikin mutane dubu ke cikin sahun ‘masu mugun barci.’
Labari mai dadin shi ne za mu iya ganin alamu na rashin isasshen barci a tattare da su.
Amfanin binciken
Binciken da Dr Ptacek da tawagarsa suka gudanar ya nuna cewa masu yin wannan irin barcin za su fi sabawa da hakan a kan wasu.
"Muna da yakinin cewa wadannan mutane suna da koshin lafiya," a cewar mai binciken.
"Suna gajeren barci kuma suna gudanar da harkokinsu ba tare da matsala ba, saboda haka barcinsu yana da amfani a gare su. Tambayar a nan ita ce mai hakan ke nufi?"
Kamar muna kusa da amsar wannan tambaya.
A wani sabon bincike, an yi duba kan kwayoyin halitta da ke da ‘alaka da yin gajeren barci ’ tare da wasu beraye da ke dauke da cutar Alzheimer ta saurin mantuwa.
"Yana da kyau saboda yana yiwuwa mu yi amfani da ilimin halittu don samun waraka, ba kawai ga cutukan da suka shafi jijiyoyin jiki da suka daina aiki ba.
Har ma da cututtukan da suka shafi hauka da ciwon sukari da yawan kiba da kuma ciwon daji," a cewar Dr Ptacek.
Ga wasunmu da ke daukar kashi daya bisa uku na rayuwarsu don yin aiki, akwai abubuwa da dama da suka kamata mu sani a kan barci.
"Wani abu na faruwa idan muka yi barci wanda zai ba mu damar yin ayyukan mu cikin kuzari idan muka tashi washegari.
"Idan muka dauki lokaci don sanin alfanun samun adadin barci da ake bukata, hakan zai yi tasiri mai kyau ga lafiyarmu."