Me ya sa ƴanbindiga ke yawan garkuwa da ɗalibai a jami'ar Dutsin-Ma?

Asalin hoton, FUDMA
Duk da cewa BBC ba ta samu alƙaluma a hukumance na yawan ɗalibai da ma'aikatan jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina, bayanan da BBC ta samu sun nuna jami'ar na ɗaya daga cikin waɗanda ƴanbindiga suka mayar karkatacciyar kuka mai ɗaɗin hawa.
Ko a ranar Lahadin da ta gabata sai da ƴanbindigar suka yi garkuwa da wasu ɗalibai guda huɗu ƴan jami'ar a wata unguwa da ake kira Paris inda ɗaliban jami'ar ke zama.
A watan Yunin 2024 ƴanbindiga sun kashe Dakta Tiri Gyan David na jami'ar sannan suka yi awon gaba da ƴaƴansa guda biyu waɗanda sai da aka biya maƙudan kuɗi kafin a sake su.
Me ya sa ake yawan satar ɗalibai a jami'ar?
"Ba a cikin jami'ar ake satar ɗalibai ba. A unguwannin da suke zaune ne a nan ƴanbindigar ke zuwa su sace su. Saboda mazaunin jami'ar na dundundun da ke wajen garin Dutsin-Ma ba zai zaunu ba saboda matsalar tsaro." In ji wani malamin jami'ar da bai so a ambaci sunansa ba.
A yanzu haka dai jami'ar na aiki ne daga wata tsohuwar makarantar sakandire da ke garin na Dutsin-Ma inda kuma mazauninta na dundundun da ke ɗauke da ofisoshi da ɗakunan ɗalibai ke nesa da garin mai nisan kimanin kilomita 27 daga Dutsin-Ma.
"Idan da ace kowa a cikin farfajiyar jami'ar yake to da wuya a samu yawan satar ɗaliban kasancewar jami'a na da katanga da ƙofar shiga sannan kuma za ta tsaurara matakan tsaro. To amma a yanzu haka da wuya a iya zama a wurin kasancewar wuri ne da ke kan hanyar Ƙanƙara/Ƴantumaki da ta zama wurin dabdalar ƴanbindiga." In ji malamin jami'ar.
Dalilai biyar da suka sa ƴanbindiga ke dabdala a Dutsin-Ma
Dakta Ibrahim Sani Ƙanƙara masanin tarihi da tsaro a jami'ar Bayero da ke Kano ya lissafa wasu dalilai guda biyar da ya ce su ne suka sa jami'ar ta Dutsin-Ma ta yi ƙaurin suna wajen sace ɗalibai musamman a baya-bayan nan.
- Kasancewar Dutsin-Ma a kan hanyar ƴanbindiga: Shi kansa garin na Dutsin-Ma yana tsakanin garuruwan Ƴantumaki da Ƙanƙara da ke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina.
- Sasanci da ƴanbindiga: Sasancin da aka yi da ƴanbindiga a yankin Birnin Gwari na jihar Katsina ya sa masu ɗauke da makaman sun koma ƙaddamar da hare-hare a yankunan da ba a cimma sulhun da su ba kamar Dutsin-Ma da ke jihar Katsina. Haka kuma farmakin da sojoji ke kai wa ƴan bindigar a yankunan Sokoto da Zamfara shi ma na taka rawa wajen kora su zuwa yankunan jihar Katsina.
- Ƙarancin jami'an tsaro da rashin kayan aiki: Kamar yadda aka sani, Najeriya na fama da ƙarancin jami'an tsaro sannan inda akwai jami'an tsaron ma ba su da kyan aiki. Ƴanbindiga suna sane da cewa akwai matsala saboda haka da sun samu dama sai su kai farmaki musamman idan suka samu bayanai daga masu kwarmata bayanai da ake kira infoma.
- Masu kwarmata bayanai: Yawanci ɓarayin nan na daji ba sa kai hari hakan nan har sai sun samu bayanai daga masu kwarmata bayanan da ake kira infoma. Kuma waɗannan mutanen a cikin al'umma suke zaune. Lallai sune matsala babba ta wannan rashin tsaro.
- Rikici tsakanin ɗalibai da ƴan sintiri: Wannan ka iya zama dalili na baya-bayan nan inda mako guda kenan da aka samu wani rikici tsakanin ƴan sintiri da ɗalibai sakamakon harbe wani ɗalibi da ƴan sintirin suka yi bisa zargin ɗalibin da ƙin bin dokar hanya. Hakan ne ya janyo janyewar ƴan sintirin daga aiki har zuwa ƴansanda su kammala bincike. To su kuma ɓarayin daji sun yi amfani da wannan dama suka kutsa suka sace ɗalibai.
'Muna cikin zaman zulumi a Dutsin-Ma'
Duk da cewa halin tsaron da jami'ar ke fuskanta bai firgita ɗalibai sun bar jami'ar ba, amma akwai yanayi na zaman zulumi da rashin tabbas.
"Gaskiya muna cikin yanayin fargaba kasancewarmu a nan. Idan banda muna da imani kan ƙaddara mutum ba zai zauna ba. Ko ɗalibai ma a tsora ce suke amma kuma hakan bai hana ɗalibai neman jami'ar ba." In ji wani malami.
Dangane da yadda ɗalibai ke tururuwar shiga jam'air ta Dutsin-Ma, ma'aikacin jami'ar ya ƙara da cewa "a bana mun ɗauki ɗalibai kimanin dubu 10 kuma ma akwai waɗanda ba su samu nasarar shiga jami'ar ba. Ka ga kenan idan gwamnati za ta samar da cikakken tsaro a makarantar to ina mai tabbatar maka yaran da za su shigo makarantar nan Allah ya yi yawa da su."











