Yadda 'Turji ya kafa sabuwar daba' a wani yanki na Sokoto

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Al'ummar Sabon Birni a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce riƙaƙƙen ɗan bindiga Bello Turji yana nan a ƙauyukansu, inda ya ke ci gaba da garkuwa da mutane da sanya masu haraji.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin ƙasar ke cewa tana bibiyar Turjin kuma nan ba da jimawa ba za ta ga bayan sa.

Al'ummar yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoton sun ce yanzu haka Bello Turji ya kafa sabuwar daba a yankinsu, inda ya ke tura yaransa su aikata ɓarna a ƙauyukan yankin.

Sun ce Turji da yaran nasa sun dawo da kai hari kan ƙauyuka ne bayan janyewar sojojin Najeriya da a baya suka yi ɓarin wuta a maɓoyar ƴan bindigar.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Sabon Birni ta arewa a majalisar dokokin jihar Sokoto, Aminu Boza, ya shaida wa BBC cewa dama can suna zaune ne a hali na rashin tabbas.

''Cikin faɗan da aka yi, shi Bello Turji, an kashe masa yaro kuma makamansu sun ɓata. Saboda haka sun je garin Baushe, ɗaya daga cikin ƙauyukanmu da ke gabashin Sabon Birni, kilomita uku daga Sabon Birnin Local Government.

"Sun ɗauki mutum 13 har da limami a lokacin da ake sallah, sun kuma je wani ƙauye sun ɗauki mutum biyar, kuma sun sanya kudi naira 250,000 kan kowanne, sannan suka sanya wa garuruwa naira miliyan 25 na mutuminsu da aka kashe da kuma makaman da aka lalata masu.

Boza ya ƙara da cewa ''mutanen ba su da kudin biya, don haka suka haɗa kansu suka samu Turji. Sau uku suna zuwa. ko yau Chairman nasu ya kira ni ya ce akwai wani sabon wakili da Bello Turji ya naɗa domin karɓar kuɗi a hannunsu, kuma mutumin ya same su ya gabatar da kansa''.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ɗan majalisa Aminu Boza ya bayyana irin matakan da suke ganin ya kamata a ɗauka domin gaggauta samar wa jama'a sauƙin matsalar.

''Abin da muke so ga gwamnatin tarayya shi ne ta bayar da umarni ga sojoji su shiga daji su yi faɗa da ƴan ta'addar nan domin gamawa da su'' in ji Boza.

Dangane da ƙoƙarin da majalisar dokokin jihar Sokoto ke yi domin ganin gwamnati ta yi abin da ya dace kuwa, Boza ya ce ''Duk abin da ya kamata a yi mun yi, har abin da ba mu nemi gwamna ya yi ba ya yi. Ko shekaran jiya gwamnoni sun je sun samu shugaban ƙasa da kuma ministocin tsaro. Shi ma mataimakin gwamna ya gana da babban hafsan sojin Najeriya, amma har yanzu babu wani abin da ya canza.''

BBC ta yi ƙoƙarin jin ta bakin hedikwatar tsaron Najeriya a kan wannan batu, amma muƙaddashin kakakin hedikwatar, Group Captain Bukar Ali Ibrahim, wanda aka kira ta waya, ya aiko da saƙon cewa yana wani aiki kuma ba zai iya magana ba, sannan bai bayar da amsar saƙon da aka aika masa da bayanin dalilin kiran sa a waya ba.

Amma a wata hira ta daban da gidan talabijin ɗin Channels, babban jami'in tsare-tsare na hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya jaddada cewa dakarun Najeriya suna bibiyar kai-komon Bello Turji, kuma nan ba da jimawa ba za su ga bayan shi.

Dama dai rundunar sojin Najeriya ta sha jaddada cewa ta kusa ganin bayan Turji, wanda ya yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane da neman kudin fansa a jihohin Zamfara da Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya.