Ahmed Musa ya yi ritaya daga buga wa Najeriya wasa

Ahmed Musa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ahmed Musa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasan Najeriya wanda a tarihi ya fi kowane ɗan wasan ƙasar yawan cin ƙwallaye a Gasar cin Kofin Duniya, Ahmed Musa ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasar wasa.

Musa, wanda tarihi zai daɗe yana tuna shi sanadiyyar gudumawar da ya bai wa ƙasar ya ce: "na yanke shawarar daina buga wa ƙasata wasa, wanda ya kawo ƙarshen shekara 15 da na yi tare da ƙungiyar Super Eagles," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na sada zumunta.

Ahmed Musa ya buga wa Najeriya wasanni 111 ya bayyana taka wa Najeriya wasa a matsayin "abin da ya fi masa komai".

Ya buga wa Najeriya wasanni a matakin ƴan ƙasa da shekara 20 da ƴan ƙasa da shekara 23 da kuma babbar tawagar Najeriya ta Super Eagles.

"Zama mutumin da ya fi kowa buga wa Najeriya wasa a tarihin ƙwallon ƙafa babbar karramawa ce gare ni," in ji Musa a cikin sanarwar da ya fitar.

Ya ƙara da cewa "duk lokacin da na sanya rigar Najeriya, na san nauyin da ya rataya a kaina. Na yi iyakar bakin ƙoƙarina a lokacin da abubuwa ke tafiya yadda ya kamata da kuma akasin haka, domin buga wa Najeriya ba abu ne na ƙashin kaina ni kadai ba.

'Abubuwan da nake alfahari da su'

Ahmed Musa na murna bayan cin ƙwallo a karawa tsakanin Najeriya da ƙasar Iceland lokacin gasar cin kofin duniya da aka yi a ƙasar Rasha a shekarar 2018

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ahmed Musa na murna bayan cin ƙwallo a karawa tsakanin Najeriya da ƙasar Iceland lokacin gasar cin kofin duniya da aka yi a ƙasar Rasha a shekarar 2018

Tsohon kyaftin ɗin na Najeriya ya kuma tuna da wasu muhimman abubuwa da suka faru da shi a tsawon lokacin da ya kwashe yana yi wa Najeriya wasa.

"Lashe gasar cin kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2013 na ɗaya daga cikin manyan abubuwa.

"Zura ƙwallo a ragar ƙasar Argentina da kuma Iceland a gasar cin kofin duniya abubuwa ne da ba zan taɓa mantawa ba. Kasancewa na jefa ƙwallo hudu a gasar kofin duniya da kuma zama ɗan wasan Najeriya da ya fi kowa zura ƙwallo a gasar abu ne da nake matuƙar godiya a kai.

"Zama kyaftin Super Eagles ma na ɗaya daga cikin abubuwan da ba zan manta ba a wannan tafiya tawa," in ji Musa.

Tsohon kyaftin din na Najeriya ya bayyana zama jagoran ƴan wasan a matsayin abin da ya koya masa darussa masu yawa, kamar jagoranci da haƙuri da kuma rashin nuna son kai.

'Na cimma burina'

Rigar Ahmed Musa mai lamba bakwai

Asalin hoton, Getty Images

A cikin sanarwar tasa, Ahmed Musa ya gode wa abokan wasansa da ƴan kallo da kuma masu horaswa bisa "amincewa da shi da suka nuna".

"Yayin da na zo ƙarshen wasannin da na buga wa Najeriya, zan yi hakan ne cikin kwanciyar hankali da gode (wa Allah).

"Na san cewa na yi bakin ƙoƙarina, kuma na san cewa Super Eagles za ta ci gaba da samun nasara," in ji tsohon ɗan wasan na Najeriya.